Hukumar Ƙwallon Ƙafar Kudancin Amurka (Conmebol) ta gabatar da buƙata a hukumance ta ƙara yawan ƙasashen da za su halarci Gasar Kofin Duniya ta 2030 zuwa ƙasashe 64.
Haɗakar ƙasashen Sifaniya da Morocco da Portugal ne za su karɓi baƙuncin gasar, bayan buɗe ta a ƙasashen Argentina da Paraguay da kuma Uruguay.
- Matar da aka haifa ‘babu mahaifa’ ta haihu
- Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan mutuwar Fafaroma Francis
Gasar Kofin Duniya ta 2026 ce ta farko da ƙasashe 48 za su halarta, to amma Conmebol na son a faɗaɗa gasar ta 2030 domin murna cika shekara 100 da fara gasar.
“Hakan zai bai wa ƙasashen duniya damar kallon gasar, don haka ba wanda za a bari a baya dangane da bikin da za a yi na cika shekara 100 da fara gasar,’’ a cewar Shugaban Conmebol, Alejandro Dominguez a wani taro da hukumar ta gudanar makon jiya.
“Mun yarda cewa bikin cika shekara 100 na gasar zai zama ƙasaitacce, saboda ba a taɓa yin irin sa ba’’, in ji shi.
Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Uruguay, Ignacio Alonso ne ya fara gabatar da buƙatar a lokacin taron FIFA da aka gudanar a cikin watan Maris.
Cikin wata sanarwa da hukumar FIFA ta fitar ta ce, haƙƙinta ne ta yi nazarin kowace shawara da mambobinsu suka gabatar.
Shugaban Hukumar ta FIFA ta, Gianni Infantino ya halarci taron Conmebol na ranar Alhamis, inda kuma ya bayyana cewa, Gasar 2030 za ta zama ‘’gagaruma’’ da ba a taɓa gani ba.
A shekarar 2017 aka ɗauki matakin faɗaɗa ƙasashen da za su halarci gasar 2026 zuwa 48 bayan duka mambobin FIFA sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da matakin.
A ranar 15 ga watan Mayu mai zuwa ne za a gudanar da taron FIFA na 75, kuma a nan ne za a tattauna buƙatar ta Conmebol.
Idan har aka amince da buƙatar, gasar ta 2030 za ta ƙunshi karawa 128, daga karawa 64 da ake yi tsakanin 1998 zuwa 2022.
Masu sukar matakin dai na cewa, faɗaɗa gasar zai rage darajar tsarin da ake bi wajen tantance cancantar shiga gasar, yayin da Kungiyar Kare Muhalli ta FFF ta ce, shawarar buga gasar a nahiyoyi uku “barazana ce ga muhalli”.
Tuni dai a farkon watan nan Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Turai, Aleksander Ceferin ya bayyana matakin a matsayin ‘’mummunar shawara’’.
“Wannan shawara ta yiwu ta fi ba ni mamaki fiye da ku, ni ina ganin wannan shawara ce maras kyau a ra’ayima,” in ji Ceferin a wani taron manema labarai.
Za dai a fara gasar 2030 a Uruguay – ƙasar da ta fara lashe gasar a 1930, a wani ɓangare na bikin cika shekara 100 da fara gasar.