Hukumar Ƙwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta ce za ta faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata daga tawagogi 32 zuwa 48.
FIFA ta ce sabon tsarin zai fara aiki ne daga gasar 2031, wadda Amurka ce kawai ke neman ɗaukar nauyinta.
- Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso
- HOTUNA: An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya
Tuni dai FIFA ta faɗaɗa gasar cin Kofin Duniya ta Maza da za a yi nan gaba, zuwa wannan adadi.
FIFA ta ce ta ɗauki matakin ne saboda yadda gasar ke ci gaba da samun karɓuwa da farin jini tsakanin masoya ƙwallon ƙafa a duniya.
Masu suka sun zargi hukumar da fifita kuɗin da za ta samau fiye da la’akari da yawan wasanni da ’yan wasa za su fuskanta.