Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta dakatar da tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya Luis Rubiales shekaru uku.
Rubiales ya sumbaci ’yar kwallon Sifaniya, Jenni Hermoso a leɓe bayan wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta mata da Sifaniya ta doke Ingila a Sydney.
- ‘Ya kamata matasa su jagoranci gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya a Najeriya’
- Mutum 14 sun mutu, 50 sun jikkata a hatsarin jirgin kasa a Indiya
Hermoso ta ce ya sumbace ta ba tare da amincewarta ba, hakan ya haifar da ce-ce-kuce, inda a ƙarshe Rubiales ya sauka daga muƙaminsa a watan Satumba.
Daga baya Hermoso ta shigar da ƙara a kan Rubiales.
A ranar Litinin FIFA ta sanar da dakatar da Rubiales na tsawon shekaru uku saboda karya dokar da’a ta 13 ta dokokinta.
Ta tabbatar da lamarin ya shafi “abubuwan da suka faru a lokacin wasan ƙarshe a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ranar 20 ga watan Agustan 2023, wanda aka dakatar da Mista Rubiales na wucin gadi na tsawon kwanaki 90”.
Rubiales na da damar ɗaukaka ƙara idan har bai amince da hukuncin da aka yanke masa ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Agustan da ya gabata ne FIFA ta dakatar da Luis Rubiales daga matsayinsa na Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Sifaniya kan sumbatar Jenni Hermoso.
Daga bisani bayana an yi ta cec-kuce kan lamarin, Rubiales ya nemi afuwa kan cewa ya riƙe gabansa ne a lokacin da yake murna a bangaren mayan baki wato VIP na filin wasan Sydney, yayin da Sarauniya Letizia ta Sifaniya da ’yarta mai shekara 16 ke tsaye kusa da shi.
Daga farko dai ya nemi kare kansa kan abin da ya aikata, yana mai cewa ya yi ƙoƙarin jajanta wa Hermoso ne bayan golan Ingila Mary Earps ta kama fanaretin da ta buga.
Sai dai daga baya Rubiales ya ajiye mukaminsa mako uku bayan an zarge shi da sumbatar ’yar wasan ba tare da izininta ba.
Rubiales ya sanar da sauka daga mukaminsa ne a wata sanarwa da ya fitar yana mai cewa ba zai iya ci gaba da rike mukamin ba a Hukumar Kwallon Kafar Sifaniya (RFEF) sannan daga bisani ya tabbatar da cewa ya mika takardar ajiye aiki ga shugaban riko na hukumar Pedro Rocha.
Haka kuma, Rubiales ya sauka daga matsayinsa na mataimakin shugaban hukumar kwallon kafar Turai UEFA.