✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan wasan Super Eagles suka kunyata ’yan Nijeriya

Ga dukkan alamu sai Nijeriya ta sake shiri muddin tana son samun gurbi a Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Ayarin ’yan wasan Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa, Super Eagles sun kunyata ’yan Nijeriya a wasan neman gurbin zuwa gasar cin Kofin Duniya, inda ’yan wasan Jamhuriyyar Benin suka doke su da ci 2-1 a wasan da suka buga a Abidjan a ranar Litinin ta makon jiya.

Kungiyar Super Eagles ce ta fara cin kwallo a minti na 27 da fara wasan ta hannun Raphael Onyedika.

To sai dai minti 10 kacal ’yan wasan Benin suka farke ta hannun Jodel Dossou, sannan Steve Mounie ya kara ta biyu ana daf da zuwa hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon Benin, wadda ita ce ta 97 a teburin FIFA, ta koma ta daya a Rukuni na Uku da maki bakwai, sai Lesotho ta 149 a teburin FIFA ke biye da ita da maki biyar, yayin da Rwanda ta 131 a teburin FIFA ta zama ta uku da maki hudu.

Afirka ta Kudu wadda ita ce kasa ta 59 wajen iya taka leda a duniya, ita ce ta hudu da maki hudu.

Sai babbar yaya Nijeriya wadda ita ce kasa ta 30 a teburin FIFA ta zama ta biyar da maki uku yayin da Zimbabwe wadda ita ce kasa ta 122 a teburin FIFA take karshe a rukunin da maki biyu.

Nijeriya ta dai ta sha kunya ne a hannun tsohon kocinta Mista Gernot Rohr, wanda ya fara aiki da ita a Agustan 2016.

Rohr ya fara wasa da kafar dama a wannan gasa da cin wasan farko inda ya doke Tanzaniya a Uyo.

Ya fara rashin nasara ranar 10 ga watan Yuni a hannun Afirka ta Kudu da cin 2-0.

Ranar 7 ga watan Oktoban 2017, shi ne na farko daga Afirka da ya samu gurbin zuwa gasar cin Kofin Duniya a Rasha a shekarar 2018 lokacin yana kocin Nijeriya.

Haka kuma Rohr ya ja ragamar Super Eagles zuwa mataki na uku a gasar cin Kofin Afirka a shekarar 2019, kafin a kore shi a ranar 12 ga watan Disamban 2021.

An kuma sallame shi ne duk da ya kai Nijeriya gasar cin Kofin Nahiyar Afirka a shekarar 2021 da karawar cike gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya.

Wannan wasa da ƙasashen Nahiyar Afirka ke bugawa don neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Kanada da Meziko, ga dukkan alamu sai Nijeriya ta sake shiri, domin duk wadda za ta je gasar tilas ta zo ta ɗaya a rukunin da take daga cikin rukunoni tara da aka raba nahiyar.

Ko kuma in ta ci sa’a ta kasance a cikin kasashe hudu da za su buga wasan cike gurbi don kaiwa ga gasar cin Kofin Duniyar.

Idan za a iya tunawa wasanin da Super Eagles ta buga duka ta tashi kunnen doki ne, sai wanda Benin ta doke ta da ci 2-1.

Misali a ranar 16 ga watan Nuwamban 2023 Nijeriya ta yi kunnen doki da ci 1-1 da kasar Lesotho, sai ta sake yin kunnen doki da Zimbabwe da ci 1-1 a ranar 19 ga Nuwamban, 2023, sannan ta sake yin kunnen doki da Afirka ta Kudu da ci 1-1 a nan gida Nijeriya.

Sai kuma a ranar Litinin da ta gabata Benin ta doke tad a ci 2-1.

Wasannin da suka rage wa Super Eagles

Ranar 17 ga Maris 2025: Rwanda da Nijeriya

Ranar 24 ga Maris 2025: Nijeriya da Zimbabwe

Ranar 31 ga Agustan 2025: Nijeriya da Rwanda

Ranar 7 ga Satumban 2025: Afirka ta Kudu da Nijeriya

Ranar 5 ga Oktoban 2025: Lesotho da Nijeriya

Ranar 12 ga Oktoban 2025: Nijeriya da Benin.