✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arsenal ta gasa wa Madrid aya a hannu

Mikel Merino ya zura ƙwallo ta uku a minti na 75 da take wasa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta lallasa Real Madrid a daren nan a karawar da suka yi ta kwata-fainal a Gasar Zakarun Turai.

Arsenal dai ta doke Real Madrid da ci 3-0 a fafatawar da suka yi a filin wasa na Emirates da ke Landan.

An kammala minti 45 na karawar babu ci, sai dai alƙaluma sun nuna Arsenal ta kai farmaki sau huɗu yayin da Real ta kai hari sau biyar.

Duk da cewa babu ɓangaren da ya samu nasarar zura ƙwallo amma wasan wanda Irfan Peljto na ƙasar Bosnia Herzegovina ya yi alƙalanci ya yi matuƙar zafi tsakanin ɓangarorin biyu.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne ɗan wasan tsakiya na Arsenal, Declan Rice ne ya zura ƙwallon farko a minti na 58 ta hanyar bugun tazara bayan da ’yan wasan Madrid suka yi wa Bukayo Saka ƙeta.

A minti na 70 ne Declan Rice ya ƙara zura ƙwallo ta biyu a ragar Real Madrid ta hanyar bugun tazara kamar yadda ya yi a karon farko.

A yayin da aka ci gaba da ɗauki ba daɗi ne Mikel Merino ya zura ƙwallo ta uku a minti na 75 da take wasa, bayan ɗan wasa Lewis Skelly ya zuro masa ƙwallon daga gefe.