✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AC Milan ta ɗauki Luka Modric

A watan Mayu Modric ya sanar da cewa zai bar Madrid bayan shafe kaka 13 a Sfaniya.

Ƙungiyar AC Milan da ke Italiya ta tabbatar da ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Real Madrid, Luka Modric.

Ƙungiyar ta Serie A ta ce ɗan wasan ya sanya hannu ne kan yarjejeniyar shekara ɗaya tare da zaɓin ci gaba da taka mata leda a shekara ta biyu wato zuwa 2027.

Modric mai shekara 39 zai yi ƙoƙarin farfaɗo da AC Milan bayan fuskantar ƙalubale a kakar da ta gabata wanda a yanzu kulob ɗin ke gyaran fuska gabanin soma kakar bana.

Modric na kasar Croatia wanda ya taba lashe kyautar gwarzon ɗan wasan duniya ya isa Milan inda kuma aka tabbatar da koshin lafiyarsa tare da samun kyakkywar tarba daga wasu gomman magoya bayan ƙungiyar.

Modric ya isa AC Milan a jiya Litinin, kwanaki 5 bayan wasansa na ƙarshe da Real Madrid.

Tun a watan Mayu dai Modric ya sanar da cewa zai bar Madrid bayan shafe kaka 13 a Sfaniya.

Ya lashe kofuna 28, da suka haɗa da Gasar Zakarun Turai shida da Kofin Duniya na ƙungiyoyin ƙwalon ƙafa guda shida da UEFA Super biyar da kofin La Liga huɗu da Copa del Ray biyu da kuma Spanish Super Cup biyar.

AC Milan dai ta ƙare ne a matsayi na takwas a teburin Serie A a kakar da ta gabata kuma ba ta samu gurbin taka leda ba a gasar Turai.