✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko Barcelona za ta lashe La Liga a ranar Lahadi?

Yanzu dai daga ranar Lahadi za a tantance lokacin da Barcelona za ta dauki kofin nan.

Ranar Lahadi Espanyol za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan mako na 34 a La Liga.

Kungiyoyin biyu sun tashi 1-1 ranar 31 ga watan Disamba a Camp Nou a karawar farko a kakar bana ta La Liga.

Da yake wasan na hamayya ne watakila a ranar Barcelona za ta lashe babban kofin tamaula na Sifaniya.

Rabon da Barcelona ta lashe La Liga tun kakar 2018/19, mai kofin 26 jimilla, amma Real Madrid ce mai rike da na bara.

Kawo yanzu idan aka buga wasannin mako na 34 a karshen mako, zai rage saura fafatawa hudu a karkare kakar bana, wato make 12 ne a kasa daga ranar ta Lahadi zai rage.

Barcelona tana mataki na daya a kan teburi da maki 82 da tazarar maki 13 tsakani da Atletico Madrid ta biyu mai maki 69.

Real Madrid ce ta uku da maki 68, sai Real Sociedad mai maki 61 ta hudu a kan teburi.

Barcelona za ta iya lashe kofin tun kan ranar Lahadi, idan Atletico Madrid ta kasa cin Villareal ranar Asabar 13 ga watan Mayu.

Haka kuma Barcelona za ta iya daukar La Ligar tun kan ranar Lahadi, idan har Real Madrid ba ta iya doke Getafe ba ranar Asabar.

Haka kuma koda Barcelona za ta kasa cin wasan da suka rage mata, ya zama wajibi Atletico da Real Madrid su lashe sauran wasannin La Liga da ke gabansu.

Hakan zai yi wahala Barcelona ta bari wannan damar lashe La Liga ya sullube mata,

Yanzu dai daga ranar Lahadi za a tantance lokacin da Barcelona za ta dauki kofin nan.