Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sama da mutane 40 ciki har da ma’aikatan kiwon lafiya aka kashe a harin da aka kai wani asibiti da ke Sudan a ƙarshen mako.
Ofishin hukumar ta WHO da ke Sudan, ya ce daga cikin waɗanda suka mutu akwai ƙananan yara shida da jami’an kiwon lafiya biyar, sannan kuma an yi wa ginin asibitin mummunar ɓarna.
- EFCC ya kama manyan jami’an NNPC kan badaƙalar Dala 7.2bn
- Yarjejeniyar tsagaita wutar Isra’ila da Iran ta samu tasgaro
RFI ya ruwaito cewa an dai kai harin ne kan Asibitin Al Mujlad da ke a yammacin Kordofan a ranar asabar da ta gabata, kusa da inda ake fafatawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, a yaƙin da suke yi tun a watan Afrilun shekarar 2023.
Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya nemi a dakatar da kai wa cibiyoyin kiwon lafiya hari, duk da cewa bai ambaci sunan ɓangaren da ake zargi da kai wannan hari ba.
Sai dai ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun zargi wani jigin yaƙin sojojin Sudan marar matuƙi da kai wannan hari, da wata sanarwa da aka fitar a ƙarshen mako ta ce mutunen da suka mutu sun kai 9.