Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta yi duk mai yiwuwa domin bankaɗo tushen ɓullar cutar coronavirus da kuma dalilin fantsamarta a sassan duniya.
Shugaban hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana hakan yana cewa duk da faɗi-tashin ƙwararru, har yanzu ba su da wani cikakken bayani kan abin da ya hana su cimma buri kan binciken da suke gudanarwa.
Cutar Coronavirus na cikin cutukan da suka fi gigitar da duniya, wadda ba za’a taɓa mantawa da ita a duniya ba, la’akari da yadda ta yi sanadin mutuwar miliyoyin mutane, da kuma tilasta sanya dokar hana shige da fice, matakin da ya tsayar da duniya cak.
An dai fara samun ɓullar cutar a yankin Wuhan na ƙasar China a ƙarshen shekarar 2019, duk da dai ƙasar ta musanta hannu a ɓarkewar cutar.
A 2021 ne Tedros ya ƙaddamar da wani kwamitin ƙwarraru kan kimiyya don su gudanar da bincike kan yadda cutar ta samo asali da kuma yadda cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta fantsama ko ina a duniya.
Sai dai ya ce duk da wasu kwamitocin da aka kafa bayan wannan aka kuma dora musu alhaki iri ɗaya amma har yanzu an gaza gano ko da dalilin ɗaya gamsashe abin da ke zama tamkar almara.
A cewarsa, abinda aka iya ganowa da kuma tabbatarwa kawai shi ne cewa cutar ta tsallaka jikin ɗan adam ne daga wasu dabbobi, amma babu tabbacin waɗanne nau’in dabbobi ne kai tsaye.