Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur ta je har gida ta yi wa Manchester City dukan kawo wuƙa da ci huɗu da nema.
Tottenham ta fara jefa ƙwallonta ne ta hannun ɗan wasan tsakiyarta, Maddison a minti na 13.
- Gwamnonin PDP sun bayar da wa’adin shirya babban taron jam’iyyar
- Na yi wa mahaifina alƙawarin ba zan taɓa aikata masha’a ba — Murja
A minti na 20 Maddison ya sake jefa ƙwallo ta biyu a raga, lamarin da ya sa Tottenham a gaba.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Pedro Porro ya jefa ƙwallo ta uku a raga s minti na 52.
A minti na 93 ɗan wasan gaban Tottenham, Johnson ya ƙarƙare da ƙwallo ts huɗu a raga.
Yanzu haka Manchester City ta yi rashin nasara a wasanni biyar a jere s kowace gasa.
Yanzu haka dai matsin lamba zai ƙars kaimi a kan kocin ƙungiyar, Pep Guardiola.
Rashin nasarar na zuwa ne, bayan da Guardiola ya sake rattaba hannu kan ci gaba da zama a Manchester City.
Yanzu haka Manchester City na mataki na biyu a teburin Gasar Firimiyar Ingila da maki 23 daga wasanni 12.
Liverpool ce ke kan gaba a teburin gasar da maki 28 daga wasanni 11 da ta buga.
Ita kuwa Tottenham na mataki na shida da maki 19 daga wasanni 12 da ga buga a gasar.