Cikin watan Agusta za a fara kakar Premier League ta 2024/25, sai dai tun kan nan wasu ‘yan kwallon na jinya.
Kungiyoyin da za su kara a gasar bana da dama sun je Amurka da sauran kasashe domin yin atisayen tunkarar kakar bana.
- Yadda ake kwashe shekaru ana shari’o’in kisan gilla a Nijeriya ba a gama ba
- Manchester City ta doke Man United a kofin Community Shield
Tuni kuma wasu na yin cefane don kara karfin kungiyoyin a fafatawar da ake ganin za ta yi zafi matuka.
Manchester City ce mai rike da kofin Firimiyar Ingila, wadda sai a ranar karshe aka tantance mai kofin tsakaninta da Arsenal, wadda ta yi ta biyu.
Cikin wasannin atisayen tunkarar kakar bana da ake yi, Newcastle United da Everton su ne ke da ’yan wasa shida-shida da ke jinya.
’Yan wasa biyar ne a Manchester United ke jinya ciki har da sabon mai tsaron baya da ta dauka a bana, Leny Yoro, wanda ya ji rauni a wasa da Arsenal.
Ga wasu ’yan wasa da ke jinya kamar yadda muka kalato daga BBC.
Arsenal
Kieran Tierney
Takehiro Tomiyasu
Aston Villa
Boubacar Kamara
Chelsea
Moises Caicedo
Nicholas Jackson
Everton
Jarrad Branthwaite
James Tarkowski
Iliman Ndiaye
Idrissa Gueye
Leicester City
Jamie Vardy
Liverpool
Andy Robertson
Curtis Jones
Manchester United
Tyrell Malacia
Leny Yoro
Rasmus Hojlund
Marcus Rashford
Antony
Tottenham
Richarlison
Fraser Forster
Destiny Udogie