✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid za ta kece raini da Osasuna a wasan karshe na Copa del Rey

Sau 19 Madrid tana lashe kofin na Copa del Rey, karo na karshe a shekarar 2014.

Real Madrid za ta kara a wasan karshe da Osasuna a filin wasa na La Cartuja a kokarin lashe kofin Copa del Rey.

Wasan na karshe zai wakana ne yayin da Madrid ke taga-taga a gasar La Liga.

Wannan shi ne karon farko da Osasuna take harin lashe wani babban kofi.

Sau 19 Madrid tana lashe kofin na Copa del Rey, karo na karshe a shekarar 2014.

Osasuna na fatan samun kwarin gwiwa daga magoya bayansu 25,000 don ganin sun dauki wani babban Kofi a karon farko a tarihinsu na shekara 103.