✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kalamai kan mata: Wacce ta caccaki Sheikh Daurawa ta ba da hakuri

Matar nan mai amfani da shafukan sada zumunta da ta caccaki fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ta fitar da sabon bidiyo…

Matar nan mai amfani da shafukan sada zumunta da ta caccaki fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ta fitar da sabon bidiyo inda ta nemi afuwar malamin.

A farkon makon nan ne dai matar, mai suna Nafisa Ishak, tare da sauran masu amfani da shafukan da dama suka caccaki malamin bisa wasu kalamai da ya yi a kan al’aurar mata, lamarin da suka ce bai dace ya fito daga bakinsa ba.

Tun da farko dai Nafisa ta fitar da sakon bidiyon ne a makon da ya gabata, inda ta bayyana rashin jin dadinta tare da sukar malamin bisa yadda ya yi bayanin.

Sai dai kuma a ranar Alhamis, ta sake fitar da sabon bidiyon bayar da hakuri bisa ga yadda ta fahimci malamin da kuma irin matakin da ta dauka a kai, tana mai bai shi hakuri tare da dukkan wadanda ta bata wa rai dangane da  maganarta a kan shi.

“Ina bai wa kowa da kowa hakuri a kan kuskuren da na yi, ban yi domin na aibata malam [Daurawa] ba,” inji ta.

Har ila yau, ta kuma jaddada nadamarta a kan yadda ta soki malamin sakamakon yadda ta ce mutane ba su gamsu da ba da hakurin da ta yi a sakon muryar da ta fara fitarwa kafin bidiyon ba, “Malam Allah Ya huci zuciyarka”.

Da ma tun  bayan bullar bidiyon na suka da ta yi ta fara fuskantar Allah wadai daga wajen magoya baya malamin kan yadda ta soke shi kai tsaye, lamarin da wasu ke ganin hakan ne ma ya sa ta fitar da sabon bidiyon, amma ba don ta sauya ra’ayinta kan kalaman malamin ba.

A cikin makon da ya gabata ne dai  fitaccen malamin  ya yi bayani a wani karatunsa kan gudun duniya, inda a ciki ya ce duk da mata na daga cikin abubuwan jin dadin duniya; to al’aurarsu da mafi yawancin mutane suke fifitawa ta fi komai muni a halittar tasu, shi ya sa Allah boye ta ba tare da bayyanar da ita a fuska domin jan hankalin mutane ba.

’Yan Kannywood sun goyi bayan Sheikh Daurawa

Maganar ta Shehin Malamain ta tayar da kura a kafafen sadarwa, inda ita Maryam Ishak ta ragargaji malamin a wani bidiyo da ta fitar.

Sai dai binciken Aminiya bai gano yadda ta zama jaruma ba, domin Aminiya ba ta samu gano wani fim da ta fito ba, kuma ba a samu wata alakarta da fim ba.

Maganar Maryam ta bar baya da kura, inda aka yi ta ce-ce-ku-ce a kafafen sadarwar zamani a tsakanin masu kare ta da masu zagin ta.

Ba a bar Masana’antar Kannywood ba a wajen batun, inda fitaccen furodusa, Alhaji Sheshe ya bude fili da wani dogon rubutu, inda a ciki ya caccaki Maryam.

Alhaji Sheshe ya ce, “Muna Allah-wadai da kalaman wannan shaidaniyar a kan Malam Aminu Daurawa. Malam mene ne hukuncin masu zagin wani malami?

“Hukunci na farko Annabi (SAW) ya ce mutuwar malami mutuwar dukkan halittu ne hatta abin da ba ya motsi kamar bishiyoyi saboda muhimmanchin malamai ya sa Annabi (SAW) ya fadi haka.

“Annabi ya ce wani lokaci yana nan zuwa da al’ummata za su raina malaman kirki su watsar da su suna musu kallon banza sai Allah Ya jarrabe su da masifu uku.

“Za su yi ta yin sana’a babu albarka. Ma’ana ba wai babu samu ba, amma za ka ga mutum nemansa na karuwa wahalarsa da dogon buri suna yi masa yawa ba ya da hutun da talaka yake da shi hatta matarsa ba ta da lokacinsa. To wannan arzikin babu komai cikinsa sai wahala saboda an cire albarka a ciki.

“Allah zai rika ba su shugabanni azzalumai marasa tausayin talakawa kuma su rasa yadda za su yi da su.

“Za su rika mutuwa a Musulunci amma suna cikawa babu imani saboda talauci ya sa su sabon Allah barkatai… Allah Ya sa mu dace Ya ganar da mu hanya madaidaiciya.”

Shi ma jarumi Ali Nuhu ya yada wani rubutun da darakta Nura Mustapha Waye ya yi, inda a ciki yake cewa, “Duk wanda ya san martabar addini, ba zai zagi malaman addini ba, saboda su ne suke koya mana bin Allah da ManzonSa.”

Tuni ake cewa Hukumar Hisbah tana neman Maryam bisa kalaman nata ga Sheikh Daurawa, duk da cewa Aminiya ba ta samu tabbacin haka ba.

A wani bangaren kuma, an fara cewa ta nemi yafiyar Shehin Malamin kan cin zarafinsa da ta yi.