Minitsan harkokin wajen Jamhuriyyar Nijar, Hassoumi Massoudou ya ayyana kansa a matsayin Shugaban Gwamnati, yana mai kira ga al’ummar kasar su murkushe juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohammed Bazoum.
Kawo yanzu dai ba a san hanlin da Mista Bazoum yake ciki ba a hannun masu juyin mulkin. Amma wani sako da aka wallafa ta shafinsa na Twitter a safiyar Alhamis ya ce, “za a kare nasarar da ya samu” kuma al’ummar kasar ne za su tabbatar da hakan.
- Sau 240 aka fasa bututun man Najeriya a mako guda —NNPC
- NAJERIYA A YAU: Shin da gaske NLC za ta iya shiga yajin aiki kuwa?
A ranar Alhamis ake sa ran sojojin su sanar da wanda zai jagoranci gwamnatin tasu, amma wani makusancin Bazoum ya bayyana wa kafar yada labaran Farasa cewa juyin mulkin ba zai yi tasiri ba.
Zargin kashe madugun juyin mulki?
Wasu rahotanni daga kasar kuma na cewa sojojin sun kashe wanda ya jagorance su wajen yin juyin mulkin, Abdulrahman Chani.
Shugaban gidan rediyon Amfani FM da ke birnin Yamai na kasar, Issoufu Mammane, ya shaida wa Aminiya cewa ana zargin an harbe shi har lahira ne a yayin takaddama kan wanda zai jagoranci gwamnatin sojin, wadda yake neman nada kansa.
“A yayin jayayya saboda ya ce shi zai dauki mulki, su kuma sauran sojojin suka ce ba shi zai dauka ba ga wanda za ya dauka (Salifou Modi)… suna wannan jayayya ne wani ya ciro bindiga ya harbe shi,” a cewar Malam Issoufu Mammane.
Kawo yanzu dai Aminiya ba ta iya tabbatar da faruwar hakan ba.
Har yanzu dai masu juyin mulkin ba su sanar da sunan wanda zai jagoranci gwamnatin da suka kafa ba, wanda hakan ya sa ake ta hasashe.
Juyin mulki: An rufe iyakokin kasar Nijar
Sojojin kasar Nijar da suka yi juyin mulki dai sun jingine kundin tsarin mulki tare da dakatar da daukacin hukumomi da cibiyocin gwamantin kasar.
Bayan tabbatar da kifar da gwamnatin Bazoum, kakakin sojojin, Kanar Manjo Ahmadou Abdrahamane, ya kuma sanar da rufe duk iyakokin kasar da kuma hana zirga-zirga a cikin kasar daga karfe 10 na dare zuwa 7 na safe.
Sojojin sun sauke daukacin ministoci daga mukamansu, don haka manyan sakataron ma’aikatun ne za su ci gaba da gudanar da su.
Kannar Manjo Ahmadou Abdrahamane, ya kuma bukaci kasashen waje da kada su tsoma bakinsu a cikin wannan al’amuri na cikin gidan kasar Nijar.
A cewarsa, sojojin sun kifar da gwamantin Bazoum ne saboda matsalar tsaro da karancin ababen more rayuwa da kuma koma-bayan tattalin da suka addabi kasar.
A wane hali Bazoum yake?
Sai dai kuma a hannu guda, minitsan harkokin waje na kasar, Hassoumi Massoudou ya ayyana kansa a matsayin Shugaban Gwamnatin kasar, yana mai kira ga al’ummar kasar da su kawo karshen juyin mulkin da sojojin kasar suka yi wa Shugaba Mohammed Bazoum.
Amma kawo yanzu dai babu wani bayani game da halin da Mohamed Bazoum yake ciki a hannun sojojin da ke tsare da shi ba.
Hakazalika babu bayani game da ko ya amince ya ajiye mukaminsa, ballantana na makomarsa.
Yuyin mulki a yankin Sahel
Yanzu Nijar ta zama kasa ta hudu a fadin yankin Sahel — wadandan dukkansu rainon Farasan ne — da baya-bayan nan sojoji suka yi juyin mulki.
Nijar, daya daga cikin kasashe matalauta a Afirka, na fama da matsalar masu ikirarin jihadi nau’i biyu a yankin Kudancin kasar. Yakin Kudu maso Gabas na fama da ta’addancin Boko Haram da ISWAP da ta gangaro daga Arewa maso Gabashin Najeriya. A yankin Kudu maso Yamma kuma matsalar ta gangaro ne daga kasar Mali tun shekarar 2015.
Kasashe biyar na yankin (Nijar, Chadi, Mali, Burkina Faso, Mauritaniya) da Najeriya sun kafa kungiyar G5 Sahel domin yakar ta’addanci, a yayin da suke fama da masu da’awar jihadi, kamar yadda Najeriya ke fama da Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas.
Ba za mu lamunci juyin mulki ba — ECOWAS
Kungiyar raya tattalin arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya yake jagoranta ta ce ba za ta lamunci karin juyin mulki a Nijar ko wata kasa a yankin ba.
Tuni ECOWAS ta tura tawaga ta musamman karkashin Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyar Benin domin shiga tsakani.
A ranar Alhamis ake sa ran tawagar ta ECOWAS za ta gana da bangaororin bangarorin biyu da nufin sasanta rikicin.
Juyin mulki a Nijar
Yunkurin juyin mulki na karshe a kasar shi ne wanda aka yi a jajibirin rantsar da Mista Bazoum a shekarar 2021.