✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sau 240 aka fasa bututun danyen man Najeriya a mako guda —NNPC

An gano haramtattun layuka 93 da barayin suke jan danyen mai daga bututun NNPC a jihohin Ribas da Delta da Bayelsa

Kamfanin Mai na Najeiya (NNPCL) ya ce sau 240 barayi suka fasa butun danyen mai a sassan kasar a cikin mako guda da ya gabata. 

Kamafnin ya ce fasa bututu da satar danyen mai sun kara kamari a yankin Neja Delta musamman jihohin Ribas da  Bayelsa da Delta, inda aka gano aka kuma toshe wurare 93 da barayin suka jona fayif suna satar mai daga bututun gwamnati.

NNPC da jami’an tsaro sun kuma gano wurare 27 da barayin suka fasa bututun domin kwasar danyen mai, wanda a halin yanzu kamfanin ke aikin gyaransu.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce duk da cewa an gano tare da lalata haramtattun matatun mai 69 a cikin wata guda da ya gabata, matsalar tsaro a bangaren danyen mai zai kawo karin koma-baya ga tattalin arzikin Najeriya.

Ta ce a mako guda da ya gabata, an kama akalla jiragen ruwa na katako guda 30 da manyan motoci da ake amfani da su wajen safarar man sata da dai sauran laifuka.

Sai da kuma kamfanin bai ambaci komai game da matakin da aka dauka a kan mutanen da ke da alaka da jiragen da kuma haramtattun matatun ba.

Tattalin arziki zai yi kasa – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya yi hasashen tattalin arzikin Najeriya zai samu cikasa a sakamakon matsalar tsaro a bangaren man kasar.

Rahoton da IMF ya fitar a ranar Talata ya nuna matsalar za ta kawo nakasu ga cigaban kasar a shekarun 2023 da 2024.

A cewar rahoton farashin danyen mai zai karye a 2023, wanda hakan zai shafi tattalin arzikin Najeriya mai dogara a kan bangaren.