✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Juyin Mulki: Ba mu yarda Tinubu ya tura sojoji Nijar ba — Majalisar Dattawa

Muna da shugabannin kasa, wadanda sojojin Nijar ke mutuntawa kamar Buhari da Abdulsalam.

Majalisar Dattawa ta ki amincewa da bukatar neman goyon bayanta da Shugaba Bola Tinubu ya aika kan tura sojoji zuwa Nijar, don tilasta wa sojojin da suka yi juyin mulki a kasar komawa kan tsarin dimokuradiyya.

Aminiya ta ruwaito cewa, Shugaba Tinubu ya nemi goyon bayan ’yan majalisar ne cikin wata wasika da ya aika musu ranar Juma’a.

A cikin wasikar, Tinubu ya bayyana wa majalisar matakan da ya dauka a matsayinsa na shugaban Kungiyar ECOWAS ta raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma.

Bayan fitowa daga wani zaman sirri a ranar Asabar, Majalisar ta jaddada goyon bayanta ga yunkurin ECOWAS, sai dai ta ce sam babu maganar amfani da karfin soja.

“Mun ki amincewa saboda ba abu ne da ya kamata a fara tunaninsa ba ma, saboda abu ne na cikin gida,” kamar yadda Sanata Ali Nudme ya shaida wa manema labarai.

Sanatan ya kara da cewa shawarar da mafi yawan sanatocin suka bayar ita ce a ci gaba da yunkurin sulhu ta hanyar difilomasiyya, maimakon karfin soja.

“Muna da shugabannin kasa, wadanda sojojin Nijar ke mutuntawa kamar Buhari da Abdulsalam da Babangida da Jonathan, idan aka yi amfani da wadannan za a samu masalaha,” a cewarsa.

Haka kuma, cikin wata sanarwar da Shugaban Majaliisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya fitar, ya yi kira ga Shugaba Tinubu a matsayinsa na shugaban ECOWAS da ya hada kai da sauran shugabannin kungiyar ta ECOWAS da su mayar da hankali kan tsarin siyasa da diflomasiyya da sauran hanyoyin wajen warware tankiyar da ta dabaibaye Jamhuriyar Nijar.

Sanata Akpabio ya ce a dauki matakai kan yadda za a shawo kan lamarin “ganin cewa akwai kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar.”

Cikin matakan da Tinubu ya dauka akwai kulle iyakokin Najeriya da Nijar, da katse wutar lantarkin da kasar ke samu daga Najeriya, da dakatar da huldar kasuwanci, kamar yadda ECOWAS ta cimma a zaman da ta yi a Abuja.