✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun kashe masunta 8 a iyakar Kamaru da Najeriya

Mayakan Boko Haram sun yi garkuwa da masunta da dama.

Kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād da aka fi sani da Boko Haram ta kashe masunta takwas a wani hari da ta kai a Arewa maso Gabashin tafkin Chadi da ke kan iyakar Kamaru da Najeriya.

‘Yan ta’addan na Boko haram da ake zargi mayakan Bakoura Buduma ne sun kai wa masunta hari a wani yanki mai nisa da ke kusa da tsibirin Kofia a Kamaru a ranar 2 ga Agusta, 2023.

Bayanai sun ce mayakan Boko Haram sun haramta wa jama’ar yankin kamun kifi da noma tun bayan nasarar kai hare-hare da rundunar sojin Saman Najeriya ta yi wanda ya yi sanadin kashe ’yan ta’adda da dama ciki har da manyan kwamandoji.

Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi cewa, an yi musu yankan rago ne bayan da aka zarge su da yin leken asiri tare da tsallakawa cikin yankunan da ake zaton sun boye.

Majiyar ta ce bayan kashe mutane takwas, sun kuma yu garkuwa da masunta da dama a cikin kwale-kwale kusan 8, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 5 duk jirgi daya da mutanen da ke cikinsa.

Garkuwa da mutane da safarar makamai da satar shanu da kuma sanya haraji kan manoma da makiyaya da masunta na karuwa a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a yankin na Tafkin Chadi.