Wasu ’yan bindiga kimanin 30 sun sheka lahira a wani luguden wuta da jiragen sojin Najeriya suka yi musu a yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
Jiragen sun jefa wa ’yan bindigar bom ne a yankin Kwiga-Kampanin Doka da ke Birnin Gwari bayan samun bayanai kan shirinsu na kai hari.
Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Edward Gabkwet ya ce, “Jiragen yaki sun gano su ne a wani wuri da suka taru, inda aka jefa musu bom, aka hallaka mafi yawansu.”
Edward Gabkwet ya bayyana cewa an gano dandazon ’yan ta’addan ne a kan baburansu a lokacin da suke kan hanyarsu ta kai hari, aka jefa musu bom aka kashe.
- Yau Tinubu zai rantsar da kwamitin karin albashi
- Magidanci ya yi dambe da ’yan bindiga a gidansa a Kaduna
Jami’in ya ce ’yan bindigan da jiragen suka kashe din ne suka addabi Karamar Hukumar Birnin Gwari, inda suka kai wa sojoji harin kwanton bauna a yankin Kwanar Mutuwa a ranar Asabar.
A cwearsa, ’yan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne a hannun dakarun rundunar soji ta Operation Whirl Punch.