✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magidanci ya yi dambe da ’yan bindiga a gidansa a Kaduna

Maharan sun yi awon gaba da matarsa da ’ya’yansa ba sun ba hamata iska a yankin Birnin Gwari, kuma ya ki bin su

Wani magidanci ya yi dambe da ’yan bindiga a lokacin da suka je domin yin garkuwa da shi a kauyen Kidandan da ke yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Da misalin karfe 2 na dare kafin wayer garin Litinin ne ’yan bindigar suka shiga kauyen suna harbi, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin zullumi.

Wani shaida a kauyen ya ce maharan, “Sun yi kokarin tafiya da shi da karfi, amma suka kasa, saboda haka suka tafi da matarsa da ’ya’ya uku, shi kuma aka kai shi asibiti daga basani.”

Shaidu sun ce maharan sun yi nufin yin garkuwa a mijin matar ne, amma ya ba hamata iska da su, ya kwaci kansa, inda a garin fadan suka ji masa rauni.

Mai unguwar Kidandan, Alhaji Abubakar Umar Ruka, ya tabbatar da harin, sai dai ya ce ba shi da masaniyar ko duka yaran da aka tafi da su matar ce mahaifiyarsu.

Kokarin wakilimu na jin bayani daga kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ci tura domin jami’in bai amsa kira da sakon da aka aika masa ba.