✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ciyamomin Borno za su fara sa hannu a rajistar zuwa aiki

Za a tsige duk shugaban karamar karamar hukuma da ke fashin zuwam ofis

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya wajabta wa shugabannin kananan hukumomi sanya hannu sau hudu a kullum a wurin aiki.

Gwamnan ya ce yin hakan ya zama wajibi ne domin gwamnatinsa ba za ta lamunci fashin zuwa aiki, ko makara ko kuma tashi kafin cikar lokaci daga ciyamomin ba.

Da yake jawabi a wurin bikin rantsar da su a ranar Litinin, Zulum ya ce, “Duk shugaban karamar karamar hukuma da ya yi fashin zuwa ofis za a tsige shi.

“Da gaske nake! Dole ne kowannensu a dauki hoton yatsunsa sau hudu a kowace ranar aiki domin mu san cewa ya zo ofis.

“A baya na sha yi musu magana cewa kowannensu ya koma karamar hukumarsa saboda an samu zaman lafiya amma sun ki.”

A cewar gwamann kullum sai sun sanya hannu a rajistar zuwa aiki da karfe 8 na safe, 12 na rana, 2 na rana da kuma karfe 3:30 nara rana, lokacin tashi daga aiki.

Zuluma ya ce za a sanya na’uarar daukar bayanai da hoton yatsun ma’aikata a daukacin sakatariyoyin kananan hukumomi 27 da ke jihar.

A safiyar Litinin ne gwamnan ya rantsar da sabbin ciyomomin kananan hukumomi 27 da kansiloli da masu ba shi shawara na musamman guda 29 da kuma manyan sakatarori bakwai.

Gwamnan ya ce ya sha samun rahoton cewa wasunsu sun tare a otel a Maiduguri, babban birnin jihar, ba su san halin da al’ummarsu suke ciki ba.

A cewarsa, a halin yanzu an samu kwanciyar hankali a Borno, saboda haka, “Kada waninku ya kawo min uzurin cewa ba zai iya zuwa wani yanki ba saboda tsoron an dasa bom.

“Shi ya sa tun a lokacin yakin zabe ’yan takara sai da muka fada cewa duk wanda ba zai iya shiga kowane lungu a karamar hukumarsa ba, to ya hakura.”

Game da zargin rashin sakin kudaden kananan hukumomi, Zulum ya ce, “a watanni shida da suka wuce, babu karamar hukumar da ta samu kudi kasa da Naira miliyan 400.

“Saboda haka duk wani kwamishina ko ciyaman da ke korafin cewa ba a sakin kudin kananan hukumomi yana iya sauka daga kujerarsa.”