Mazauna Unguwar Salanta da ke yankin Gadon Kaya a jihar Kano sun koka kan yadda Hukumar Tsara Birane (KNUPDA) ke yunkurin rushe musu gidaje.
Mazauna unguwar sun bayyana cewar tsawon kwanaki sun rasa samun kwanciyar hankali sakamakon yadda hukumar ta goga musu jan fenti mai nuna alamar su kwana da shirin a koda yaushe aikin rusau zai biyo ta kan gidajen nasu.
- Kashi 99 cikin 100 na satar danyen man fetur ya rataya a wuyan sojoji — Dokubo
- Babbar Sakatariyar Hukumar FIFA Fatma Samoura za ta yi murabus
Da yake bayani ga manema labarai, daya daga cikin mazauna unguwar, Aliyu Adakawa ya bayyana cewar a yanzu haka ba sa iya barci da su da iyalansu, domin kuwa a kullum matasa na shigowa unguwar domin diban ganima.
Ya ce sun je neman jin bahasi a Hukumar ta KNUPDA amma sai shuganta ya shaida musu cewar su ma umarni suka samu daga sama.
A cewarsa, suna da dukkan takardun da suka halasta musu wadannan wurare, kuma suna rokon gwamnati da ta girmama ka’idar da ta shimfida na mallakar fili.
Ana iya tuna cewa, gwamnatin Jihar Kano ta yi alkawarin rushe dukkan wuraren da aka sayar ko a gina ba bisa ka’ida ba, ciki har da filayen makarantu, asibitoci, ganuwar Kano, makabartu da sauran wuraren da ba su kamata ba.
Sabon Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na dai zargin tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje da siyar da wurare mallakin gwamnati ba bisa ka’ida ba ciki har filayen da ake zargin na Makarantar Fasaha ta Polytechnic da ke unguwar ta Salanta.