✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashi 99 cikin 100 na satar danyen man fetur ya rataya a wuyan sojoji — Dokubo

Ka ambaci sunayen sojojin da ke wannan aika-aikar.

Tsohon jagoran tsagerun Neja Delta, Asari Dakubo ya yi zargin cewa kaso 99 cikin 100 na harkallar satar danyan man fetur ya rataya a wuyan sojojin kasa ne da takwarorinsu na ruwa.

Dakubo Asari na wadannan kalamai ne a yayin wata ganawa ta musamman da  Shugaba Bola Ahmed Tinubu ranar Juma’ar a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja.

Yayin ganawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala tattaunawar, Dakubo Asari ya ce Shugaba Tinubu ya yi alkawarin gudanar da bincike game da wannan zargi, musamman kan rundunar sojin ruwan kasar.

Dakubo Asari ya kuma kara da cewa ya zama wajibi gwamnati ta jajirce la’akari da karfin da masu wannan sata ke da shi, inda ya ce yana da kwarin gwiwar nan ba da jimawa ba, za a fara ganin mutane suna layi zuwa gidan yarin Kuje.

‘Ka ambaci sunayen sojojin da ke wannan aika-aika’

Sai dai kuma bayan wannan zargi, rundunar sojin ruwa ta kalubalanci Dokubo kan ya bayyana sunayen sojojin da suke satar man.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce babu wata hujja da Dakubo ya rika wajen yin wannan zargin kawai dai yana kokarin kare kansa ne matsayinsa na tsohon mai laifi.

Da yake martani, mai magana da yawun rundunar sojin ruwan, Commodore Adedotun Ayo-Vaughan, ya bayyana kalaman Dokubo a matsayin kazafi marar tushe.

Adedotun ya bayyana cewa masu satar man fetur sun fusata ne saboda matsin lambar da suke fuskanta musamman daga dakarun sojin ruwa wajen hana su gurgunta tattalin arzikin kasar.

Ya tunasar da Dokubon cewa, a halin yanzu akwai ayyukan da rundunar sojin ruwan ta kaddamar tun watan Afrilun bara wanda ta yi wa lakabi da ‘Operation Dakatar da Barawo’ domin yi wa tufkar hanci dangane da matsalar satar man fetur a yankin na Neja Delta.

Ya nanata cewa rundunar sojin tare da hadin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin sun toshe duk wata kafa da barayin danyen man fetur za su yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.