Jakadan Faransa a Jamhuriyar Nijar, Sylvain Itté, ya fice daga birnin Yamai da asubahi zuwa kasar Chadi inda daga nan ya hau jirgi zuwa kasarsa.
Sylvain Itté ya bar Nijar ne kamar yadda sabuwar gwamantin sojin Nijar ta hakikance, saboda gwamantin kasarsa ta soki juyin mulkin da suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yuli.
- Gwamnatin Kano za ta yi karar alkalin zaben gwamna kan cin mutuncin Kanawa
- An kama barayi 2 da wayoyin sata 1,000 a Kano
Wata majiyar jakadancin Faransa ta ce, “jakadan da wasu abokansa shida sun bar birnin Yamai ne da misalin karfe 4 na asuba.”
Zuwansa Chadi kafin samun jirgi zuwa gida na da alaka da haramta wa jiragen Faransa shawagi a sararin samaniyar Nijar da gwamatin sojin kasar ta yi.
An shafe makonni ana nuna wa juna yatsa dakanin gwamnatin sojin Nijar da Faransa, babbar kawar gwamantin Bazoum, wadda sojojin suka hambarar a ranar 26 ga watan Yuli.
Da farko sojojin sun tube wa jakadan rigar kariya tare da soke bizarsa, suka ba shi wa’adin ficewa daga kasar cikin kwana biyu, amma har wa’adin ya kare bai tafi ba, yana cikin ofishinsa.
Gwamnatin sojin ta kuma dage cewa dole sai sojojijn Faransa da ke kasarsu su tafi, amma Faransa ta ce ba su isa ba, tunda su ba halastacciyar gwamanti ba ne.
A ranar Lahadi ne dai Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya sanar cewa Mista Sylvain Itté da jami’an ofishin jakadancin kasar a Nijar za su dawo gida.
Ya kara da cewa cikin makonni masu zuwa kasar za ta rufe aikin sojinta a Nijar ta kuma kwaso sojojinta kafin karshen shekara.
A cewar Macron duk da cewa gwamantin sojojin Nijar ta hana jiragen kasarsa shawagi a sararin samaniyar Nijar, bangarorin biyu za su tattauna kan ficewar dakarun nasa daga Nijar.
Sojojin Nijar sun yi maraba da hakan, inda suka bayyana cewa wajibi ne a ayyana ranar da dakarun na Faransa za su kammala ficewa daga Nijar.
Sun kuma sanar da cewa suna tsara matakan da za a bi domin ficewar ta kasance bisa fahimtar juna.