✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano za ta yi karar alkalin zaben gwamna kan cin mutuncin Kanawa

Gwamnatin Kano ta ce zagin masu jar hula cin mutuncin Malam Aminu Kano da Kanawa ne, don haka ba za ta lamunta ba.

Gwamnatin Kano ta yi barazanar maka Mai Shari’a Benson Anya, daya daga cikin alkalan kotun zaben gwamnan jihar, kan zargin sa da cin mutuncin magoya bayan Jam’iyyar NNPP da kuma tafiyar siyasar Kwankwansiyya.

Hakan na zuwa ne mako guda bayan alkalan kotun ta bakin shugabanta, Mai Shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, sun yi ittifakin soke zaban Gwamna Abba Kabi Yusuf, suka ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris, 2023.

A jawabinsa a kundin hukuncin, Mai Shari’a Benson Anya ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagorantar gwamnatin kama-karya wadda jami’anta da magoya bayanta ke barazana ga bangaren shari’a.

Da yake tsokaci game da barazanarsu ga alkalan kotun, Mai Shari’a Anya ya kira magoyan bayan NNPP “masu jar hula”, “’yan tashin hankali”, “’yan ta’adda” da kuma “wadanda aka kayar”.

Gwamnatin jihar ta bakin Kwmaishinan Yada Labaranta, Baba Halilu Dantiye, ta ce kalaman Mai Shari’a Anya kan masu sanya jar hula kadai ba, “zagi ne ga Malam Aminu Kano, wanda ya assasa sanya jar hula a Kano, da ma Kanawa masu kishi.”

Dantiye, ya ce babu yadda za a yi “alkalin ya zo har Kano ya ci mutuncin Malam Aminu Kano. Za mu bi duk hanyoyin da da suka dace don ganin an hukunta shi kan abin da ya aikata.

“Mun san hukuncin kotun batacce ne, don haka za mu ci gaba da sama wa Kanawa romon dimokuradiyya, babu abin da zai sa mu yi kasa a gwiwa wajen cika alkawuran zaben da muka yi musu.

“Tuni dama Gwamna ya umarci lauyoyinmu su daukaka kara kuma muna da yakinin kotun gaba za ta dawo mana da kujerarmu,” in ji kwamishinan.

Dantiye ya ce suna son sanin ko alkalin na dan “’yancin shigar da ra’ayinsa na kashin kai wajen soke zabenmu. Majalisar Harkokin Shari’a (NJC) da sauran hanyoyi suna nan. Za mu yi karar sa.

“Ba zai yiwu alkali ya yi fake da barazanar kisa mara tushe ya sanya ra’ayinsa wajen yanke hukunci ba. Wannan ya nuna ba ka yi adalci a hukuncin da ka yanke ba,” a cewar Dantiye.

%d bloggers like this: