Sakamakon ziyarce-ziyarce zuwa asibitoci hade da tambayar wadanda abin ya shafa kai-tsaye da kuma sauran nazarce-nazarce da bin diddigi da na yi, sai na fahimci cewa, amfani da kayan da’a na da illoli ga wadanda suke amfani da su.
Irin wadannan kayan matan na iya janyo wa matan da ke amfani da su matsalolin kiwon lafiya ko zamantakewa da mazansu.
Likitoci sun bayyana irin matsalolin da mata masu amfani da kayan mata ke fuskanta da suka hada da cututtuka.
Sun kuma bayyana yadda hadin magunguna ke iya yin illa ga farjin macce, ya barnata jikin nata, musamman irin wanda a ke saka shi cikin jiki.
Kadan daga Illolin da suke haddasawa sun hada da:
1. Kaikayin gaba: Sakamakon amfani da kayan da’a, musammman ma na matsawa da na turare da wasu matan kan yi, sai hakan ya haifar musu da kaikayin gaba. Sukan matsa ko saka sinadarin kayan da’a a al’aurarsu, ko kuma turara al’aurar tasu, wanda a karshe maimakon hakan ya cim ma ruwa, ta hanyar samun biyan bukata, sai cibi ya zama kari ta hanyar samuwar kaikayin gaba, wanda idan suka zauna ba abin da za ka ga su na yi sai soshesoshe.
2. Zubar ruwa daga al’aura: Sakamakon amfani da kayan da’a na matsawa da na turare, hakan kan haifarmusu da zubar ruwa mai doyidaga al’aurarsu, wanda zai dinga bata musu dan kamfai, ka ji suna wari mai tayar da hankali.
3. Barin Ciki: Amfani da kayan mata yana kawo barewar ciki, saboda shan maganin ake ba wani ka’ida ko ma’auni, kuma wasu magungunan suna da karfi sosai da za su hana ciki zama a mahaifa.
4. Hana daukar ciki: Wasu magungunan saboda karfinsu sukan bata mahifa ko kuma toshe inda kwai ke fitowa sai ka ga macce ta kasa daukar ciki.
5. Cutar kansa: Amfani da kayan mata barkatai yakan haifar da sankarar mahaifa (uterus cancer), wadda wani lokaci za ta iya kai ga macce ta rasa mahaifarta ko kuma rayuwarta gaba daya.
6. Hawan jini ko saukar jini: Sakamakon amfani da kayan mata na sha na haifar da matsalar hawan jini ko saukarsa. Kasancewar jini hanyar tafiyar da abinci, ruwan da muka sha da magungunan da muka sha.
Don haka idan kayan matan na dauke da wasu sinadarai masu lahani ga shi jinin ko kuma aka yawaita amfani da su, sai hakan ya kawo hauhawar jini ko saukarsa.
7. Matsanancin ciwon kai: Kayan mata na janyo matsanancin ciwon kai ko zafin jiki. Wanan ba ya rasa nasaba da karfin da maganin ya musu a jini.
8. Ciwon zuciya: Amfani da kayan mata na haifar da ciwon zuciya, kasancewar magungunan da matan kan sha suna samun damar za ga jikinsu ne, ta hanyar zagaya sassan jiki da jini ke yi.
Haka kuma da ma zuciya ita take da hakkin harba jini izuwa kowane sashi na jikin dan Adam, sannan bayan jini ya gama zagaye jikin, yakan dawo zuwa zuciya.
Kamar yadda na yi bayani a sama, cewa kayan da’a na kunshe da sinadarai da suke da lahani ga jini, don haka bayan jini ya kwashi wadannan sinadarai, ya zaga jiki da su, sannan ya dawo zuwa zuciya, hakan sai ta sanya taruwar wadannan sinadarai a zuciya, inda a nan sai ka samu sun haifar da ciwon zuciya, imma a samu kumburar fatar da take ba da kariya ga zuciya ko kuma haifar da nakasu ga ita zuciyar wajen harba jini zuwa ga sassan jiki.
Ta bangaren mu’amala da zamantakewa kuma, mata kan fuskanci matsaloli kamar haka:
1. Cire wa miji sha’awar matarsa: Da zarar magunguna da aka yi wa mace kafin ta shiga gidan mijinta ya gushe, to ni’imarta za ta ragu da kashi 80% sai ta asali da take da ita ta dawo.
Shi kuma miji ba zai dinga jin tana gamsar da shi kamar da ba. Daganan sha’awa da yake mata za ta fara raguwa, idan aka yi rashin sa’a sai ma ya haifar masa da sha’awar wasu matan a waje.
2. Gusar da ni’imar mace ta asali da take da ita: Duk macen duniya, akwai ni’imar da Allah Yai mata wajen gamsar da namiji, amma irin ni’imar kayan mata na iya haifar masu da illa wajen gusar da ni’imar da suke da ita ta asali. Domin da zarar aikin wadannan magungunan ya gushe, to ni’imarta ta asali da take da ita ma za ta ragu.
3. Rashin tattali da tanadi: Mata da yawa da suka saba siyan kayan ba su da tanadi ko ttattali, don a kullum tunaninsu yadda za su samu kudin sayan kayan matan ne.
Daga Samira Bello Shinko. [email protected]