✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Ɓata-gari sun sace takardun shari’ar Ganduje a Kano

An kitsa wannan lamari ne domin sace takardun tuhumar da ake yi wa Ganduje.

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ɓata-gari sun sace takardun shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje kan tuhume-tuhumen da suka shafi rashawa da almundahanar kuɗin al’umma.

Aminiya ta ruwaito yadda wasu ɓata-gari suka yi ta’adi a Babbar Kotun Jihar Kano da ke harabar Sakatariyar Audu Bako yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da ta rikide zuwa tarzoma.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yammacin wannan Larabar, Gwamnan ya bayyana damuwa dangane da lamarin yayin da ya kai ziyarar gani da ido kan irin ta’asar da ɓata-garin suka yi a Babbar Kotun.

“Abin takaici ne matuƙa yadda maƙiyan Jihar Kano suka ɗauko hayar wasu ɓata-gari domin lalata ɗaya daga cikin gine-ginen jama’a masu ɗimbin tarihi da nufin daƙile tuhumar da ake yi wa Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje da iyalansa da hadimansa,” inji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa ɓata-garin sun lalata kusan dukkanin sassan Babbar Kotun da suka haɗa da ofishin Alkalin Alkalan jihar, lamarin da ya janyo asarar sama da Naira biliyan daya ta hanyar satar kayan ofis, lalata ofisoshi, kona motoci da sauran abubuwa.

Sanarwar ta kuma ambato gwamnan na cewa ta’asar da ɓata-garin suka yi shiryayyen lamari ne da aka kitsa da gayya domin sace takardun tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon gwamnan jihar kan zargin rashawa.

Gwamnan ya bayar da umarnin fara gyaran kotun nan take, inda kuma ya yi wa Babbar Alkaliyar Kano, Dije Aboki da manyan alƙalan kotun jaje bisa wannan ibtila’in da ya afkawa kotun.

Gwamnan wanda ya nanata cewa ɓangaren shari’a shi ne ginshikin da ke share hawayen duk wani mara gata, ya kuma ba da umarnin a gaggauta soma gyare-gyaren ginin kotun da kuma tanadar ƙarin jami’an tsaro ba tare da ɓata lokaci ba.

Abba Kabir ya yi kira ga matasa a jihar da su daina bari ana amfani da su wajen tayar da hargitsi, a maimakon hakan, su mayar da hankali wajen neman sana’o’in hannu domin samun kyakkyawar makoma tare da jaddada cewa, gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma yaba wa al’ummar jihar bisa goyon baya da haɗin kai da suke bai wa gwamnatinsa, inda ya yi addu’ar Allah Ya ƙara tabbatar da  zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata, da bunkasar tattalin arziki a jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa, Kwamishinan Shari’a, Barista Haruna Isah Dederi, da Babban Magatakardar Babban Kotun, Alhaji Abdullahi Ado Bayero, da sauran alkalan babbar kotun jihar ne suka zagaya da gwamnan harabar kotun a yayin ziyarar.

Hotunan ziyarar gani da ido da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai kan irin ta’adin da ɓata-gari suka yi wa Babbar Kotun Kano: