Wata tirela da ke ɗauke da kusan mutum 230 a cikinta ta yi hatsari a Jihar Neja, inda akalla mutum 25 suka rasu nan take.
Bayanai sun nuna motar ta yi hatsarin ne ita kaɗai a kauyen Takalafiya da ke kan babbar hanyar Yawuri a Karamar Hukumar Magama ta Jihar Neja.
- Magoya bayan NNPP sun yi zanga-zanga kan hukuncin kotu a Kano
- Gaza: Isra’ila da Hamas za su tsagaita wuta na tsawon kwana 10
A cewar Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar, Bologi Ibrahim, Gwamnan Jihar, Mohammed Umar Bago, ya damu matuka da hatsarin sannan ya bukaci direbobi su daina karya dokokin tuki.
Ya ce hatsarin, wanda aka yi ranar Talata ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a, wanda ya sa motar ta ƙwace daga hannun direbanta.
Bayanai sun nuna tirelar dai ta taso ne daga Jihar Sakkwato dauke da mutum 229, wadanda suka hada da maza da mata da kananan yara a cikinta.
Rahotanni sun ce nan take mutum 25 suka mutu, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka kuma yanzu aka garzaya da su Babban Asibitin Kontagora, inda suke samun kulawa.
Kazalika, wadanda suka rasu yanzu haka an kai gawarwakinsu dakin adana gawarwaki na asibitin na Kontagora.