An gano karin gawarwaki 13 daga cikin fasinjojin jirgin ruwan da ya kife a Jihar Kebbi.
Tun a ranar Laraba aka gano gawarwaki biyar bayan hatsarin jirgin da ke dauke da kusan mutum 200 daga Jihar Kebbi zuwa Neja.
Jirgin ruwan ya kife ne a yankin Tsohuwan Labata da ke Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi, bayan sa’o’i da fara tafiyar.
Wani mazaunin kauyen Warra, Adamu Umar Warra, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa ana sa ran masu aikin ceto za su gano karin gawarwaki.
“Jirgin ruwan ya dauki fasinjoji 180 da babura 30 kirar Bajaj. Fasinojin na hanyarsu ce ta zuwa kasuwa a Malele da ke Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja daga Kebbi, kuma hatsarin ya faru ne awanni kadan bayan tashinsu,” inji Manajan Hukumar Kula da Rafuka ta Najeriya (NIWA) a Yauri, Jihar Kebbi, Yusuf Birma.
Ya danganta aukuwar lamarin ga raunin jirgin ruwan, ya ce, “Muna ci gaba da aikin ceto kuma lamarin ya faru ne saboda lodin wuce kima —jirgin ruwan ba shi da karfin daukar fasinja 180.”
Majiyoyi sun ce baya ga fasinjojin, jirgin ruwan ya kuma dauko bahunan kasar masu hakar zinariya da wasu kayan mutane da ke hanyarsu ta zuwa kasuwar kauye.