✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hasashen muhimman abubuwan da za su faru a Kannywood a 2024

Aminiya ta yi hasashen abubuwan da za su iya faruwa a shekarar 2024 a masana’antar ta Kannywood.

Kannywood masana’anta ce da take jan hankalin mutane, musamman ma matasan Arewa kamar yadda takwararta ta Nollywood take a yankin Kudu.

Aminiya ta yi hasashen abubuwan da za su iya faruwa a shekarar 2024 a masana’antar ta Kannywood.

Habakar masana’antar

Shekaru bakwai zuwa 10 da suka wuce, masana’antar ta shiga mawuyacin hali, har wadansu daga cikin masu ruwa-da-tsaki a cikinta suka fara tunanin za ta durkushe, ganin kasuwancin masana’antar ya tabarbare matuka.

Wadansu sun koma wata sana’ar, wadansu kuma sun hada da wata.

Da dama daga cikin masu shirya fim suna da finafinai da tsoron asara ya sa suka ajiye ba su fitar da su ba.

Sai dai yanayin sauyi da ci-gaban zamani, musamman ta intanet ya sa wadansu sun dawo da karfinsu, inda a yanzu haka harkoki suke ta dawowa a hankali.

Yanzu haka za a iya cewa masana’antar ta koma kan YouTube kacokam, inda yawancin masu shirya fina-finai suka koma shirya masu dogon zango suna dorawa a tashar, inda suke samun kudi sosai.

Manyan forodusoshi irin su Abubakar Bashir Maishadda da Abdul Amart da sauransu irin su Ali Nuhu da Alhaji Sheshe duk a YouTube suke haska fina-finansu.

A da can kananan fina-finai ake haskawa a kafar, amma yanzu manyan masu shirya fina-finai sun fara komawa kafar domin cin moriyarta tare da tafiya da zamani.

Yanzu haka ana haska fim din Kamfanin FKD na Ali Nuhu mai suna Alaka a YouTube, sannan akwai fim din Gidan Sarauta da Dan Jarida na kamfanin Abubakar Bashir Maishadda da kuma Manyan Mata na Abdul Amart da sauransu.

Lura da yadda haska fina-finai a sinima ke tafiyar hawainiya da yadda ake raba riba da masu sinimomin da karancinsu, sannan da kuma cewa kyauta ake dora finafinai a YouTube, kuma ana kallo ne su biya ka, sannan kuma Hausawa sun fara gane kallo a manhajar, Aminiya na hasashen cewa badi masana’antar za ta kara bunkasa, inda za a rika samun makudan kudade daga YouTube.

Fim din Kannywood Netflix

Ranar Asabar 30 ga Disambar 2023 ce aka haska fim din Kannywood na farko a manhajar Netflix.

Netflix ce babbar manhajar da masu shirya fim ke samun makudan kudade cikin sauki.

Aminiya ta ruwaito cewa, a fina-finan Kannywood, fim din Aisha ne ya fi tara kudi a sinimar Film House da ke Ado Bayero Mall a Kano, inda ya samar da Naira miliyan 5 da ’yan kai.

Idan aka kwatanta shi da Nollywood, fim din da ya fi samar da kudi, ya samar da sama da Naira miliyan 600.

Ana samun wannan bambancin ne saboda ana kallon fina-finansu a Netflix din, bayan manyan sinimomi da suke da su a Kudu.

An fara haska fim din Mati a Zazzau na Rahama Sadau a manhajar, wanda hakan ya sa Aminiya ke hasashen za a ci gaba da karbar fina-finan Kannywood, wanda hakan zai bunkasa masana’antar.

Shigar fina-finan Kannywood Netflix zai sa forodusoshi su kara zuba kudi, sannan za a fara samun riba, wanda hakan ke nufin kara albashin da ake biyan jaruman da ma’aikatan bayan fage.

Sai dai wani hanzarin shi ne babu Hausawa ’yan Arewa da yawa a manhajar, wanda hakan ke nufin akwai bukatar tallata ta sosai.

Darakta mace

Tun a 2020 ce ya kamata jaruma Nafisat Abdullahi ta bayar da umarnin fim dinta mai suna Zainab Ali a kamfaninta mai suna Nafs Entertainment, amma hakan bai yiwu ba saboda yanayin yadda duniyar ta shiga rudu.

Sannan kuma tabarbarewar masana’antar ta sa jarumar ta yi gum game da shirin.

Jarumar ce ta dauki nauyin fim din Yaki A Soyayya da ya yi tashe sosai a 2019, wanda tun bayansa ne ta fara shirye-shiryen zama darakta a masana’antar.

Sai dai Aminiya ta gano cewa, tsohuwar jaruma Muhibbat Abdulsalam, wadda matar darakta Hassan Giggs ce, ta riga ta zama mai bayar da umarni a Kannywood.

Nafisat ta yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje domin karo karatu da shirye-shirye.

A cikin dalilinta na ficewa daga shirin Labarina mai dogon zango na Aminu Saira, Nafisa ta bayyana rashin isasshen lokaci da karatu da kuma fim dinta da take aiki a kai a matsayin wasu daga dalilanta na ficewa daga fim din.

Kasancewar yanzu masana’antar ta fara farfadowa, sannan batun shiga Netflix da aka samu, Aminiya na hasashen a 2024 Nafisa za ta dauki fim din nata.

Sababbin jarumai za su ja masana’antar

A wani sabon lamari kuma, kasancewar an dade ana ganin fuskokin da yawa daga cikin jaruman masana’antar, sai wadansu masu kallo suke ganin lokaci ya yi da komawa YouTube ta ba da damar yin amfani da kanana da sababbin jarumai, inda fina-finai da dama sababbin jarumai ne ke jan su.

Wannan ya sa Aminiya ta rairayo wadansu jarumai da take ganin za a fi jin su a badi.

Mommee Gombe

A yanzu haka za a iya cewa jaruma Mommee Gombe ce take jan zarenta a Kannywood wanda ta fara tun bayan fitowarta a bidiyon wakar Jarumar Mata tare da mawaki Hamisu Breaker.

Ita ce take jan fim din Alaka na Ali Nuhu da Gidan Sarauta na Abubakar Bashir Maishadda sannan tana cikin Manyan Mata na Abdul Amart da sauran manyan fina-finai.

Aminiya tana hasashen za ta ci gaba da tashe a 2024.

Rukky Alim

Sunanta na asali Rukayya Ahmed Aliyu, amma an fi saninta da suna Rukky Alim a Kannywood.

Matashiyar jaruma ce da a yanzu haka ta fara jan zarenta a masana’antar.

Tana cikin fim din Alaka na Ali Nuhu da Sanda da sauransu, kuma Aminiya na hasashen za ta kara haskawa a 2024.

Amina Uba

Amina Uba wadda aka fi sani da Maman Haidar ko kuma Jamila Labarina tsohuwar matar Adam A. Zango ce.

Ta fito a Gidan Danger, yanzu kuma take jan fim din Labarina, inda ta fito a matsayin Jamila.

Aminiya tana hasashen za ta haska matuka a 2024.

Maryam Labarina

Maryam Labarina wadda aka fi sani da Ladidi domin fim din Na Ladidi, sabuwar jaruma ce da shirin Labarina ya haska sosai.

Aminiya na hasashen za a kara ganin ta a manyan fina-finai a 2024.

Zikrullah

Zukrullah a fim din Alaka ya fara haskawa, inda ya fito da sunan Khalid, amma ya taka rawar gani sosai.

Aminiya tana hasashen a 2024 za a ci gaba da ganin fuskar Zikurullah sosai.

Maryam Muhammed

Maryam ta fito a Alaka a matsayin babbar kawar Halisa.

Bayan nan ta fito a wasu finafinan da dama. Aminiya tana hasashen a 2024 ma za ta ci gaba da haskawa.