✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah za ta fara kamen mabarata a Katsina

Hukumar Hisbah za ta far kamen masu bara a fadin kananan hukumomi 34 da ke Jihar Katsina.

Hukumar Hisbah za ta far kamen masu bara a fadin kananan hukumomi 34 da ke Jihar Katsina.

Babban Kwamandan Hisbah na jihar, Dokta Aminu Usman (Abu-Ammar), ya ce hukumar za ta kori duk mabarata da ba ’yan asalin jihar ba ne zuwa jihohinsu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi yana jaddada aniyar hukumar Hisbah ta kawar da mabarata daga titunan jihar.

Dokta Aminu Usman ya ce, “gwamantin Katsina na yin duk mai yiwuwa don kawar da bara a titunan jihar, saboda bara ba ta daga cikin addinmu, sai dai ma zubar da kimar addininmu da al’ummarmu da take yi.

“Dokar da ta kafa hukumar Hisbah ta ba mu ikon bin lungu da sako mu tantance mabarata, mu gano mabukata na ainihi a cikinsu, mu mika su ga Hukumar Zakka da Wakafi domin ta tallafa musu,” in ji shi.

Shugaban na Hisbah ya ce gwamnatin jihar ta kafa hukumar Zakka da Wakafi ne musamman domin tallafa wa mabukata.

Abu-Ammar ya ce wadanda ba ’yan asalin Jihar Katsina ba ne daga cikin wadanda aka gano kuma za a mayar da su johohinsu.

Za mu sa kafar wando da masu badala —Hisbah

Sannan ya ce, hukumar Hisbah a shirye take ta yi maganin masu badala da rashin tarbiyya a jihar, don haka ya bukaci iyaye da sauran jama’a su rika kula da tarbiyyar ’ya’yansu.

Ya ce gwamnatin jihar ba za ta kara lamuntar rashin tarbiyya ba a tsakanin matasa, don haka duk wanda aka kama saboda badala, zai yaba wa aya zaki a hannun hukumomin da suka dace.

Babban Kwamandan Hisban ya ce wadanda aka kama da ba ’yan jihar Katsina ba ne kuma, za a damka su a hannun hukumomin da suka dace a jihohinsu.

“Babu mahaifin da zai so ganin matashi na shaye-shaye da sauransu, don haka muke kira ga iyaye da sarakunan gargajiya da sauran jama’a su ba mu goyon baya da hadin kai wajen cimma manufar nan ta kyautata rayuwar matasanmu,” in ji shi.

Daga nan sai ya roki al’umma da su rika fallasa bata-gari da wuraren aikata badala da ke yankunansu domin a dauki matakin da ya dace.