More Podcasts
Dangantaka na ƙara rincaɓewa tsakanin masu shirya finafinai Kannywood da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, wacce daya daga cikin jaruman fina-finan Kannywood Abba El-Mustapha, ke jagoranta.
A baya-bayan nan, hukumar ta dakatar da fina-finai masu dogon zango guda 22, bayan saɓaninta da wasu masu shirya fina-finai, inda take zargin cewa fina-finansu sun ƙetare iyaka.
Sai dai masu shirya fina-finan sun bayyana cewa sam hukumar ba ta da hurumin dakatar da waɗannan finafinai.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Kula Da Lafiyar Jikinku
- DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan rigimar da ta balle tsakanin hukumar da masu shirya finafinai masu dogon zango.
Domin sauke shirin, latsa nan