✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Mauludi: Amurka za ta taya sojojin Najeriya rage harin kuskure

Amurka ta yi wa Najeriya ta'aziyyar mutanen da jirgin soji ya kashe bisa kuskure a Kaduna

Gwamnatin Amurka ta ce a shirye take ta taimaka wa sojojin Najeriya su rage yawan harin bom bisa kuskure da sojojin kasar ke kai wa fararen hula.

Amurka ta yi wannan tayin ne bayan harin bom da jirgi mara matuki na sojin Najeriya ya kai wa masu taron Mauludi a Jihar Kaduna, inda ya kashe mutun 90, tare da jikkata wasu 66.

A ranar Alhamis ne Amurka ta sanar da cewa idan Najeriya ta ba ta dama, za ta taimaka wa sojojin kasar wasan amfani da fasahar basirar na’uara wajen kara karfin sojojin.

Cibiyar kula da makamai ta Amurka ta sanar a Abuja cewa hakan zai kuma taimaka wa sojojin Najeriya ta yadda ba za a same su da kayra dokokin duniya a yayin gudanar da aikinsu ba.

Jami’in cibiyar Paul Dean, ya kuma yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a harin da jirgin sojin Najeriya ya kashe bisa kuskure a Jihar Kaduna.

Ya shaida wa taron manema labarai cewa kasarsa a shirye take ta yaki matsalar kwararar makamai A Najeriya.