✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPP, PDP da wasu jam’iyyu 5 sun kulla ƙawancen siyasa

Jam’iyyun PDP, NNPP, SDP, APM, ADC, YPP da ZLP sun kulla kawance mai suna CCPP domin fafatawa da jam'iyyar APC mai mulki.

Jam’iyyar PDP da NNPP da wasu jam’iyyun adawa biyar sun ƙulla ƙawancen siyasa domin fafatawa da Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Jam’iyyun su bakwai sun kuma kafa gamayyyar siyasa mai suna ‘Coalition of Concerned Political Parties (CCPP)’ a wani taro da suka yi a Abuja.

Sauran jam’iyyun su ne SDP, APM, ADC, YPP da kuma ZLP.

Kawancen nasu na zuwa ne bayan tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci jam’iyyun adawa su hada karfi wajen kawar da jam’iyyar APC daga mulkin Najeriya.

Atiku ya ce hadewar na da muhimmanci domin kauce wa komawar Najeriya kasa mai jami’iyya daya. Bayan nan ne jami’iyyun adawa irinsu LP da NNPP suka ce yin hakan abu ne da ya kamata.

Ba hadewa ba ne CCPP

sai dai da yake jawabi a taron kafa kungiyar ta CCPP, Shugaban Jam’iyyar SDP na Kasa, Shehu Gabam,  ya bayyana cewa ba ba hadewa suka yi ko kafa sabuwar jam’iyyar siyasa ba.

Mukaddashin shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Umar Damagum, wanda mukaddashin sakataren jam’iyyar na Kasa, Setonji Koshoedo, ya wakilta a taron ya bayyana cewa: “Wannan gamayyar za ta samar da adawa mai kari a siyasar Najeriya. Hakkinmu ne mu samar da wani sabon mafita daga wasu tsare-tsaren gwamnati.”

Shugaban Jami’iyyar ADC na Kasa, Cif Ralph Nwosu, ya ce sun kulla kawancen ne “domin kara karfafa dimokuradiyyar kasarmu, saboda yadda muka ga jam’iyya mai muki take kokarin murkushe ’yan adawa.

A nasa bangaren Shugaban Jami’iyyar APM na kasa, Yusuf Dantalle, ya bayyana cewa akwai wasu jam’iyyu da ke cikin kawancen da ba su samu halartar taron ba.

Sauran mahalarta taron sun hada sa mukaddashin shugaban Jam’iyyyar NNPP na Kasa, Abba Kawu Ali; Sakatren Jam’iyyar YPP na Kasa, Egbeola Martins da Sakataren Jam’iyyar ZLP na Kasa.

Bukatunsu

Mukaddashin Shugaban PDP, Shehu Gabam ya yi kira da bangaren shari’a da su kara musu kwarin gwiwa kada su ba su kunya a shari’o’in da ke gaban kotuna kan zaben jihohin Kano, Zamfara, Nasarawa da Filato inda jam’iyyun adawa suka sha kaye a hannun mambobin jam’iyya mai mulki a gaban kotu.

Sun kuma bayyana damuwa kan matsalar tsaro, wadda suka bayyana cewa tana kara tabarbarewa.
Sannan suka bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta yi wa kasafin 2024 gyara, domin a cewarsu, aiwatar da abin da ke cikin kasafin ba mai yiwuwa ba.

APC ta yi gum

Har yanzu dai jam’iyyar APC mai mulki ba ta ce uffan kan kungiyar kawancen siyasar da jam’iyyun adawan suka kafa ba.

Wakilinmu ya nemi kakakin APC na kasa Felix Morka, kuma ya tura masa sakon tes da na WhatsApp, kan lamarin, amma babu amsar ko daya.

Barazana ce kawai – Farfesa Kamilu Fage

Masanin kimiyyar siyasa, Farfesa Kamilu Sani Fage, ya bayyana matakin jam’iyyun adawar a matsayin barazana da kuma gwaji.

Ya ce matakin nasu yana da nasaba da zaben 2027, amma kasancewar sai nan da shekaru uku za a shiga kakar zaben, armashin kawancen na iya mutuwa kafin lokacin, kuma APC na iya fara aiki da wuri domin rusa kawancen nasu.

Farfesa Kamilu ya kara da cewa ta wata fuskar kuma kawancen ya zo a makare, domin an yi ta neman su yi hakan kafin zaben 2023 amma ba su yi ba.

Ya bayyana cewa sakamakon zaben 2023 ya nuna ba don rabuwar kai da aka samu a PDP, da ta kayar da APC.

A cewarsa, wata matsala da kawancen siyasar za ta fuskanta ita ce ta hankokon masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 a jam’iyyun.

Fage ya kafa da cewa rashin LP na iya zama matsala, idan aka yi la’akari da yawan magoya bayan da dan takarar shugaban kasan jam’iyyar, Peter Obi, ke da shi ta fuskar kabilanci da addini a zaben 2023.

Amma ya ce duk da haka kawancen abu ne mai kyau jam’iyyun adawa sa hada kai domin magance wata matsala da ke iya tasowa.

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Clement A. Oloyede, Abbas Jimoh & Saawua Terzungwe