Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Katsina ta Arewa a Majalisar Dattijai ta Najeriya, Sanata Ahmad Babba Kaita ya yi kira da a gaggauta kawo karshen hare-haren da ake kai wa ’yan Arewa mazauna Kudancin Najeriya.
Ya yi gargadin cewa kawaicin da ’yan Arewa suke nunawa na son zaman lafiya ne ba wai na tsoro ba, ya mai cewa ya zama wajibi a kawo karshen musguna musun da ake yi.
- Cutar Murar tsuntsaye: An kashe kaji 329,556 a gidajen gona 62
- Miji ya saki matarsa saboda zanen Tinubu
Sanata Kaita wanda ya fito daga yanki daya da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kuma ce dole ne a kyale ’yan Arewa su zauna a kudu domin yin kasuwancinsu, kamar yadda suma suka kyale ’yan Kudun suna yi ba tare da hantara ba.
Sanatan na wadannan kalaman ne a cikin wani rubutu da ya wallafa mai taken, ‘Arewa: Lokacin da shiru ba zai zama masalaha ba,’ ya ce babban laifin da yanzu mutum zai aikata a Najeriya shine ya kasance dan Arewa.
“Idan aka ga kogi ba ya motsi, hakan ba yana nufin babu kadoji a cikinsa ba ne. Ja da baya ga rago fa ba tsoro ba ne; don an ji ’yan Arewa sun yi shiru ba wai don ba su da yadda za su yi ba ne ko ba su san inda yake musu ciwo ba ne,” inji shi.
Ya ce karar da ’yan Arewa suke nunawa ba ta wuce don Najeriya taci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa daya ba ce.
“Amma babu wanda bai san cewa mutunta juna abu ne da ya kamata a samu daga kowanne bangare ba, cewa gina kasa abu ne da yake bukatar kama-kama. Babu wata hamshakiyar kasa da ta wayi-gari kawai ta ganta a inda take, dole sai da mutanenta suka yi aiki,” inji Sanata Kaita.
Idan za a iya tunawa, ko a cikin makon nan sai da Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yi gargadin cewa kada ’yan Kudu su yi tunanin samun kariya a Arewa muddin suka ci gaba da kashe ’yan Arewan dake rayuwa a yankunansu.