Matan kabilar Hamar da ke kasar Habasha kan nuna bajinta kafin a aure su, ta hanyar shan bulala a bainar jama’a.
Ana gudanar da bukukuwan yi wa matan bulala ne don nuna bajintarsu a gaban samarin da za su aura tare da daure wa duk dukan da za a yi masu a gaban jama’a, kamar yadda aka dauki hoton yadda ake zane ’yan matan da za a aurar a wani rahoto da jaridar Dailymail ta wallafa.
- Ina tallan doya don tsare mutuncina —Gurgu
- Kotu ta yanke wa matashi hukuncin bulala a Kano
- Boko Haram ta yi garkuwa da Hakimi a Yobe
Wannan al’ada da ’yan kabilar Hamar a kasar Habasha ke gudanar da ita, a lokacin da ake yin duka ga ’yan matan, fatar jikinsu na dayewa saboda raunin da suke samu.
Amma suna jure wa hakan don nuna soyayyarsu ga samarin da suke son auren su.
Bayan yi musu bulalar daga bisani za su nemi taimakon wanda ya yi musu bulalar.
Zane matan da bulala wani bangare ne a cikin shagalin da maza ke yi.
A lokacin da ’yan uwan matar da za a aura ta nuna soyayyarta ga wanda take so ne za a gudanar da irin wannan al’ada a bikin.
Bayan bikin, sai saurayin da zai yi auren likafarsa ta daga ya koma matsayin cikakken namiji kuma za a ba shi damar yin auren.
Wannan al’adar gargajiya da kabilar Hamar ke yi ana kiranta da Ukuli Bula, kuma wani mai daukar hoton mai suna Jeremy Hunter ne ya yada labarinta.
A maimakon matan su tsere saboda zafin bulalar sai su ci gaba da rokon mazan su kara yi masu bulala kamar a lokacin bikin da aka gudanar a gangaren kogin Omo River Valley.
Game da yadda maza ke yin ado a ranar bikin, suna yin fenti a jikinsu, wanda ke nuna ranar ta musamman ce.
Babban abin da ake yi lokacin bikin shi ne zane budurwa a gaban jama’a, wanda ’yan uwan saurayin da zai aure ta ne za su yi wa budurwar bulalar.
Matan da aka gayyata a wajen bikin za su yi ta wakoki da busa, inda wanda ake yi wa bulalar za ta nuna juriya da bajintarta bayan yi mata bulalar.
Jikin ’yan matan da aka zane yana farfashewa saboda bulalar kuma wadansu da ake kira da MAZA ke yi wa ’yan matan bulalar.
Wadansu ’yan matan a yayin da suka gabatar da kansu don nuna bajinta suna zuwa da natsuwa don amincewa da al’adar, yayin da wadansu kuma suke zuwa da shirin a yi musu kawai su wuce.
Amma da zarar an gama yi wa budurwa bulalar sai ta samu kwarin gwiwar ta yi bajinta tare da martaba al’adar kabilarta.
Bikin al’adar na hada kan ’yan uwa da abokan arziki ta yadda mata ke nuna soyayyar da suke yi ga wanda zai aure su.
Daga bisani idan wadansu daga ciki suka zama zawarawa sai su nemi wanda ya zane su a shekarun baya don neman taimako daga wurinsa.
Zanen bulalar ko alamar dukan da aka yi musu a gadon baya na nuna sadaukarwa ce ga mijin da zai auri matar, yayin da abu ne da bai yiwuwa namijin da ya aure ta ya gaza biyan bukatar matar ko a lokacin da take bukatar agajin gaggawa.
Duk wata ’yar kabilar Hamar da ke kasan kogin Omo da ke Kudancin Habasha a shirye take ta gabatar da kanta don a yi mata bulalar al’ada ta Ukuli Bula.
Hakan na nuna gwarzantaka da karfin soyayya, kuma hakan na da alaka da wani tsarin inshora, wanda da zarar matan sun shiga cikin yanayin kuncin rayuwa bayan wasu shekaru, za su fara neman namijin da ya yi bulalar don ya taimaka musu.
Abin da maza ke yi kafin aure
Kafin namiji ya yi aure sai an yi masa abubuwa biyu na al’ada da suka hada da: Na farko sai an yi masa kaciya sannan sai ya yi wasan hawan kaho.
Hakan zai nuna bajintar namijin kabilal Hamar inda zai yi tsalle wajen hawan kahon saniya da matasan kabilar ke shiryawa.
Idan har ya yi nasarar hawan kahon – wanda zai yi tsirara, Za a iya kiran matashin Hamar a matsayin mai suna Maz (balagaggen namijin da zai iya yin aure).
Kimanin mutum 200 ne ke halartar harabar da ake bikin kabilar Hamar don nuna bajintar matan da za su yi aure.