Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta bukaci maniyyata Aikin Hajjin badi su fara ajiye Naira miliyan hudu da rabi a matsayin kafin alkalamin kudin kujera.
Shugaban hukumar, Zikrullah Kunle Hassan ne ya sanar da hakan yayin wani taro da shugabannin hukumomin jin dadin alhazai na Jihohi ranar Talata a Abuja.
- Hajjin Bana: Ƴan Najeriya sun kashe N304 Biliyan
- NNPP ta kori Kwankwaso gaba daya saboda cin amanar jam’iyyar
Ya ce kudin kujerar zai yi tashin gwauzon zabon ne sakamakon daidaita farashin da ake canzar da Dalar Amurka da Gwamnatin Tarayya ta yi a kwanakin baya, wacce yanzu haka ake canzarwa a kan kusan N750.
Sai dai ya ce farashin zai iya canzawa idan yanayin farashin Dalar ya canza kafin lokacin.
Idan za a iya tunawa, alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana na 2023 daga Najeriya sun biya Naira miliyan 2.8, a lokacin Dalar ba ta wuce N450 ba a hukumance.
Zikrullah ya ce, “Ina mai tabbatar muku cewa kudin kujerar Aikin Hajjin badi zai yi tsada sosai, ya kamata mu kwan da sanin haka tun yanzu. Ba wai na ce tun yau za mu san farashin ba, amma dai tun da wuri mu sani zai yi tsada.”
Sai dai ya ce kodayake ba yanzu hukumar za ta ya ke kudin kujerar na karshe ba, sai ya rage kwana 45 kafin ranar tsayuwar Arfa, amma tun yanzu sun riga sun fara shirye-shirye.