Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta kammala jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.
Da yake jawabi ga manema labarai a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja kafin jirgin maniyyatan ya tashi zuwa Saudiyya, Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce aikin Hajjin bana ya samu nasarori da dama da suka nuna ci gaba da inganta aikin hajjin Nijeriya.
- NDLEA ta kama maniyyata aikin hajji ɗauke da hodar iblis
- ’Yan bindiga sun kashe makiyaya 2, sun sace shanu 320 a Kaduna
Ya ce, an yi jigilar maniyyata 41,568 ta jiragen sama 105.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ya nuna matuƙar godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima bisa gagarumin goyon bayan da suka bayar wajen ganin an gudanar da aikin Hajjin 2025 cikin nasara.
A cewarsa, duk da cewa aikin jigilar jirage ba abu ne mai sauƙi ba, tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki, hukumar ta samu nasarar kammala aikin.
Shugaban Hukumar NAHCON ya bayyana cewa, akwai ƙalubale a yayin aikin jigilar jiragen amma tare da haɗin gwiwar hukumar ta samu nasarar cimma burinta na ganin duk wani mahajjatan Najeriya ya tafi ƙasa mai tsarki tare da kula da su yadda ya kamata.
“Yayin da muke rufe shirin jigilar jirage zuwa aikin Hajjin 2025 na bana daga kason jihar, wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci a gare mu baki ɗaya domin hakan na nufin mun samu nasarar kwashe dubban maniyyatanmu cikin ‘yan makonni.
“Ba abu ne mai sauƙi ba, amma da kyakkyawan tsari, bayan taimakon Allah Maɗaukakin Sarki da haɗin gwiwar da muka yi, mun kammala aiki cikin nasara, Alhamdulillah.