✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin 2025: Kashi 79 na maniyyatan Najeriya sun isa Saudiyya – NAHCON

Hukumar ta ce yanzu haka ta kwashe kashi 79 na maniyyatan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki.

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa ta yi jigilar maniyyatan Najeriya 32,549 zuwa Saudiyya don gudanar da Hajjin shekarar 2025.

Wannan adadi ya kai kashi 79.1 na jimillar waɗanda ake sa ran za su yi Hajji daga Najeriya.

Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce an kammala jigilar ne ta hanyar amfani da jirage 79 tun daga ranar 9 ga watan Mayu, 2025.

Rahoton Aminiya ya nuna cewa kimanin maniyyata 42,000 ne ake sa ran za su halarci Hajjin bana daga Najeriya.

Jihohi da dama kamar Adamawa da Filato sun kammala jigilar maniyyatansu baki ɗaya.

Jihohin Jigawa da Babban Birnin Tarayya, ana sa ran za su kammala jigilar nasu maniyyatan a yau.

Jihar Kwara, wadda ke da sauran maniyyata 137, za ta kammala kwashe su a a wani jirgi a Jihar Kano da yammacin yau.

Mahajjata daga Jihar Binuwai da yankin Kudu maso Kudu za su tashu tare a jirgi ɗaya da aka tanada da zai tashi a ranar 23 ga watan Mayu, wanda shi ne jirgi na ƙarshe daga yankin.

NAHCON, ta bayyana cewa ba a samu jirgi ko ɗaya da aka soke tashin ba tun da aka fara jigilar.

Sai dai an samu jinkirin tashin wasu jirage da gangan saboda bai wa otel-otel a Madina damar tsaftace ɗakunansu.

Wannan al’amari yana daga cikin tsare-tsaren gudanar da aikin Hajjin bana, musamman idan yawan mahajjatan ya ƙaru a lokaci ɗaya.

NAHCON, ta gode wa mahajjata da ɗaukacin al’ummar Najeriya bisa haƙuri, addu’o’i da goyon baya, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da ƙoƙarin ganin an gudanar da aikin Hajjin cikin tsari da sauƙi ga kowa.