✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsagin NNPP ya kori Kwankwaso kan ‘cin amanar’ jam’iyyar

NNPP ta kuma zarge shi da karkatar da kudadenta na kamfe

Tsagin jam’iyyar NNPP ta kasa bangaren Major Agbo, ya dakatar da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar a zaben da ya gabata, Rabi’u Musa Kwankwaso, saboda zargin cin amanarta.

Jam’iyyar ta kuma zargi Kwankwason da karkatar da kudaden yakin neman zabenta.

Korar dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na tsagin na kasa, Abdulsalam Abdulrasaq, ya fitar ranar Talata a Abuja.

Matakin na zuwa ne kwana uku bayan Major Agbu ya sha alwashin bincikar tsohon Gwamnan na Kano kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan daya da aka tara na sayar da fama-faman ’yan takara a jam’iyyar.

Abdulsalam ya ce sun dauki matakin ne bayan Kwankwason ya ki amincewa ya bayyana a gaban kwamitin ladabtarwar da ya kafa domin ya kare kansa daga zarge-zargen.

Amma Kakakin ya ce korar na kan ka’ida saboda ta dace da kundin tsarin mulkin jam’iyyar wanda aka yi wa kwaskwarima a shekara ta 2022.

Sai dai da yake mayar da martani, wani makusancin Kwankwason kuma Mai Binciken Kudi na jam’iyyar na kasa, Ladipo Johnson, ya ce tsagin ba shi da hurumin ma da zai kori tsohon dan takarar daga jam’iyyar.