Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce dole ne gwamnatinsa ta binciki tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, inda ya zarge shi da bar wa jihar abun kunya.
Da yake mayar da martani ta bakin Sakataren Yada Labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Ganduje ya rasa ta cewa ne, shi ya sa ya ɓige da batun cewar gwamnatin NNPP ta gaza a Kano.
- Sallah: Gwamnatin Tarayya ta ayyana Talata da Laraba a matsayin hutu
- Auren G-Fresh da Sadiya Haruna ya mutu
Ya ce mulkin Ganduje na shekara takwas babu abin da ya haifar face almundahana, karkatar da kuɗaɗen gwamnati da sayar da kadarorin jihar.
Gwamnan, ya ƙara da cewar wa’adin Ganduje biyu a matsayin gwamna bai taɓuka komai ba sai wawure dukiyar al’umma, zubar da jini wanda ya bar iyalan mutane cikin ƙunci.
“Watanni takwas da muka yi a kan mulki sun fi shekara takwas da Ganduje ya yi na rashin iya mulki da adalci ta ko ina,” in ji Gwamna Yusuf.
Ya shawarci Ganduje da ya yi ƙoƙarin kare “ƙimarsa” a kotu, maimakon yin maganganu marasa kan gado a kafafen watsa labarai.
Yusuf ya ce: “Tsananin cin hanci da rashawa da Ganduje tafka, ya jawo wa mutanen Kano abun kunya, kuma babu wata kafa da za ta iya ba shi kariya kan gurfanar da shi kan cin hanci da rashawa.
“Muna so mu tabbatar da ƙudurin wannan gwamnati na gurfanar da Ganduje da muƙarrabansa don su fuskanci doka kan abubuwan da suka aikata ba daidai ba,” in ji sanarwar.
Gwamna Yusuf, ya jadadda aniyar gwamnatinsa na mayar da hankali kan ci gaban zamantakewa da tattalin arziki, don ci gaban Kano da kuma al’ummar jihar.
Gwamnan, ya ce duk wani mutum da zai hana a binciki Ganduje da iyalansa kan irin badaƙalar da suka yi a Kano, ba cikakken mai kishin jihar ba ne.
Dangane da batun rashin iya shugabanci duk da ƙarin kaso da gwamnatin tarayya ke bai wa Kano, Gwamna Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa na “ƙoƙarin farfaɗowa daga gurgunta tattalin arziƙin da Ganduje ya yi wa jihar na tsawon shekara takwas.”
Gwamnan ya ƙara da cewa cin hanci da rashawa da jefa rayuwar al’ummar jihar cikin fargaba da gwamnatin Ganduje ta yi ne, ya sanya gwamnatin mai ci ta ƙirƙiro kwamiti guda biyu domin bincikar tsohon gwamnan.
Sai dai a wani martani da, Ganduje ya yi, ya ce akwai buƙatar Abba ya mayar da hankali kan yadda zai gyara tafiyarsa domin a bayyana ta ke gwamnatin NNPP ta gaza a jihar, maimakon fakewa da batun bincikarsa.