✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kori ƙarar ɗan Ganduje kan kujerar ɗan majalisa a Kano

Kotun ta ce masu karar ba su da hujja

Kotun sauraron kararrakin zabe a Jihar Kano ta yi fatali da karar da ɗan Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Umar Abdullahi (Abba) Ganduje ya shigar a gabanta.

Abba dai ya shigar da karar ce yana kalubalantar nasarar da Tijjani Abdulkadir Jobe na jam’iyyar NNPP ya samu a zaben kujerar dan majalisa a mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado daga Jihar Kano.

Alkalan kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a I.P Chima ne dai suka yi fatali da karar ranar Talata saboda rashin kwararan hujjoji daga bangaren masu kara.

Kotun dai ta ce masu shigar da karar sun gaza gabatar da kwararan hujjojin da za su gasgata zarge-zargen da suka yi a yayin zaben.

Kazalika, kotun ta umarci Abba Ganduje ya biya Jobe Naira dubu 200, saboda bata masa lokaci.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai ta ayyana Jobe a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Sai dai Abba Ganduje ya garzaya gaban kotu yana neman ta soke nasarar Joben.