✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe masu garkuwa da mutane 6 a Filato

Sojojin sun cafke wasu muggan masu kera bindigogi ta bayan fage a jihohin Filato da Kaduna.

Sojoji sun kashe wasu mutum shiga da ke garkuwa da mutane, tare da cafke wasu masu kera bindigogi ta bayan fage a jihohin Filato da Kaduna.

Rundunar sojoji ta Operation Safe Haven (OPSH) da ke jihohin ta kuma cafke wasu ’yan bindiga uku kan zargin harin kwanan nan da aka kai a kauyen Heipang da ke Karamar Hukumar Barkin Ladi da ke Jihar Filato.

Wasu mutum 54 kuma sun shiga hannun sojojin kan zargin aikata garkuwa da mutane, fashi da makami, fataucin miyagun kwayoyi da sauransu.

Kakakin rundunar Kyaftin Oya James, ya ce “Sojoji sun kuma cafke wasu muggan masu kera bindigogi ta bayan fage a Filato da Kaduna,” inda aka kwace bindigogi kirar AK-47 guda biyu da harsasai guda 55 da sauransu.

Kyaftin Oya ya ce, rundunar ta kwato wasu shanu 27 da aka sace a Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato, suka kuma cafke wasu makiyaya biyu kan zargin lalata wata gona a kauyen Yagbak da ke Karamar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.

Shi ma wani dillalin miyagun kwayoyi da ke unguwar Congo Russia a Jos, Jihar Filato ya shiga hannun sojoji.

Jami’in sojin ya ce duk wadanda aka kaman suna amsa tambayoyi a hannun masu bincike, kafin sojoji su mika su ga hukumomin da suka dace.