✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu sake bibiyar yarjejeniyar hatsi da Ukraine — Putin

Ba ma jin dadin halin da duniya ta fada saboda karancin abinci.

Rasha ta amince ta shiga wata tattaunawa da Turkiyya don sake waiwayar yarjejeniyar fitar da hatsi tsakanin ta da Ukraine da ta fice a baya.

Wannan amincewa na zuwa ne bayan da shugabannin kasashen biyu suka yi wata ganawa irin ta ta farko a bana a ranar Litinin.

Kungiyar NATO wadda Turkiya ke cikin ta, ta jima tana fatan ganin an sake dawo da wannan yarjejeniya da nufin samar da wadataccen hatsi musamman alkama a sassan duniya ciki har da nahiyar Afirka mafi bukata.

“Ba ma jin dadin halin da duniya ta fada saboda karancin abinci, amma wannan ba yana nufin muyi watsi da bukatun mu ba, za mu sake bibiyar lamarin kuma muna fatan samun matsaya mai ma’ana,” inji shugaba Putin.

Putin ya kuma kara da cewa, babu wata matsin lamba ko kuma barazana da za ta sanya shi shiga wata sabuwar yarjejeniya matukar ba za a mutunta bukatun kasar sa ba.

A watan Yulin da ya gabata ne Rasha ta ki amincewa ta sabunta yarjejeniyar fitar da hatsin da ta shiga da Ukraine na tsahon shekara guda abinda ya zamewa duniya dan zani.

Rashin mutunta bukatun da Rasha ta gabatar yayin kulla yarjejeniyar da Turkiyya ta shiga tsakanin ne dalilin da ya sanya shugaba Putin ya yi fatali da ita, sai dai a wannan karo ya nuna sha’awar sake komawa matukar dai za a biya masa wasu bukatun sa.