Tsohon Shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya magantu kan dalilin da ya zabi marigayi Umaru Musa Yar’adua a matsayin magajinsa duk da rashin lafiyar da ya yi fama da ita.
Yar’adua shi ne shugaba na biyu da ya karbi ragamar mulkin Najeriya bayan komawarta kan turbar Dimokuradiyya a shekarar 1999.
- Shugabannin ’yan kwadago sun kauracewa zama da Gwamnatin Tarayya
- Ministan Tsaron Ukraine Oleksii Reznikov zai yi murabus
Kuma Yar’adua ya karbi ragamar mulkin ne daga hannun Shugaba Olusegun Obasanjo wanda ya mulki Najeriya tsawo har karo biyu, na farko a lokacin mulkin soja daga 1976-1979 da kuma bayan komawar ƙasar mulkin dimokuradiyya daga 1999-2007.
Da yake zantawa da Jaridar Cable a ranar Litinin, Obasanjo ya musanta zargin da ake yi masa na assasa magaji mai rauni a matsayin shugaban Najeriya bayan ƙarewar mulkinsa.
Sai dai a cewarsa, ya yanke shawawar zabar Umaru Yar’adua ya zama magajinsa duk da yana da masaniyar cewa an taba yi masa dashen ƙoda.
Sai dai ya ce bayanai da kuma shawarwari da ya samu daga kwararru a fannin kiwon lafiya sun tabbatar masa da cewar duk da an yi masa dashen ƙoda, yana da ƙoshin lafiyar da zai jagoranci ƙasar nan.
“Na kafa wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin marigayi Dokta Olusegun Agagu, a ƙoƙarin neman wanda zai gaje ni.
“Sun yi la’akari da sunaye da dama, sun kuma yi nazari mai zurfi a kan su duka, sun ba da shawarar su, amma sunan Umaru ne kan gaba a jerin sunayen.
“Babbar hujjar da suka ba ni ita ce, yana da mutunci kuma ba zai saci kudin gwamnati ba. Sannan an tabo batutuwan da suka shafi lafiyarsa kuma na mika bayanan lafiyarsa wajen neman shawararar kwararrun likitoci don jin nasu ra’ayin.
“Ban bari sun san ko bayanan lafiyar waye ba don kar ma su nemi jin dalilin da nake neman shawararsu.
“Bayan sun gama nazari a kai, sun bayyana cewa ko wane ne ma da alama an yi masa dashen ƙoda, amma hakan ba abin damuwa ba ne don zai kasance cikin koshin lafiya kamar kowane mutum.
“Iyakaci ke nan. Duk zarge-zargen da ake yi na cewa na san zai mutu shi ya sa na goya masa baya ya zama shugaban kasa karya ne. Wannan shi ne haƙiƙanin labarin da na ba ku,” in ji Obasanjo.
Ana iya tuna cewa, mataimakin Obasanjo na wancan lokaci, Atiku Abubakar da kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Peter Odili, na daga cikin wadanda suka fafata wajen neman tikitin takara a jam’iyyar PDP.
Duk da haka, tsohon janar din na soji ya zabi Yar’adua, wanda kuma daga bisani ajali ya katse masa hanzari a ranar 5 ga watan Mayun 2010 yana kan ganiyar mulki.