Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa mahaifiyarsa Misis Benice Obasanjo ta ɗauki cikinsa na tsawon watanni 12 kafin haihuwarsa.
Cif Obasanjo ya alaƙanta jinkirin haihuwarsa da tasirin wasu mayu da suka bai wa mahaifiyarsa wahala kafin Allah Ya kawo mata ɗauki.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kehinde Akinyemi ya fitar ranar Alhamis a birnin Abeokuta na Jihar Ogun, ya ce tsohon shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin gabatar da wani shirin wasan kwaikwayo albarkacin cika shekaru 66 da rasuwar mahaifiyarsa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Obasanjo yana bayyana damuwa kan yadda mutuwa ta ɗauke mahaifiyarsa ba tare da ta ci moriyar ɗaukakar da ya samu a duniya ba.
Da yake jawabi yayin gabatar da shirin wasan kwaikwayon a babban laburarensa a ranar Laraba, tsohon shugaban ƙasar ya ce duk da yake ’ya’ya tara mahaifiyarsa ta haifa, amma su biyu ne kaɗai suke raye — daga shi sai ’yar uwarsa.
“Na samu labarin cewa sai da na shafe watanni 12 a cikin mahaifiyata, kuma har yanzu ba a ƙyale ni ba.
“’Ya’ya 9 ta haifa amma daga ni sai ’yar uwata muka rayu.
“A hakan ma ni kaɗai ne na samu na yi karatu saboda mahaifinmu yana kan aƙidar cewa duk karatun da ’ya mace za ta yi, a ɗakin girki za ta ƙare.”