✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo

Muddin ba a sauya tsari an dawo ana mutunta buƙatun al’ummar Afirka ba, to dimokuraɗiyya za ta mutu murus a nahiyar.

Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce mulkin dimokuraɗiyya ya gaza wajen kawo ci gaba a nahiyar Afirka.

Ya ce tsarin ya gaza ne saboda abin da ya ƙunsa bai zo daidai da al’adu, da yadda ake tafiyar da rayuwa a nahiyar ba, da abubuwan da mutanen nahiyar suka yi amanna da su ba.

Tsohon shugaban na wannan furuci ne a Abuja a wurin wani taron bikin cika shekaru 60 a duniya na tsohon mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai kuma tsohon Gwamnan Imo, Emeka Ihedioha.

Obasanjo ya buga misali da yadda tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln, ya bayyana tsarin dimokuraɗiyya da cewa gwamnati ce ta mutane da mutane ke jagoranta domin al’umma.

Ya ƙara da cewa tsari ne da ake yu domin kowa ya amfana, ba wai wani ɓangaren na al’umma ba ko wasu mutane ƙalilan ba.

Obasanjo ya kuma bayyana cewa kafin zuwan dimokuraɗiyyar ƙasashen yamma, Afirka na da nata tsarin shugabancin wanda ke kula da buƙatun kowa.

A cewarsa wannan tsarin shi ne dimokuraɗiyya, ba abin da ake kira dimokuraɗiyya ba a yau wanda ke bai wa shugabanni damar karɓar duk abin da suke so ba bisa ƙa’ida ba da kuma ta hanyar cin hanci da rashawa su ce wa mutane su je kotu idan suna da ja.

Obasanjo ya ce matuƙar ba a sake fasalin dimokuraɗiyya ta yi daidai da al’adu da manufofin ’yan Afirka da kuma mutunta buƙatun jama’a ba, to za ta ci gaba da durƙushewa kuma a ƙarshe ta mutu murus a nahiyar.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da tsoffin gwamnonin Anambra da Ribas —Peter Obi da Rotimi Amaechi.

Sauran mahalartan sun haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, tsoffin Shugabannin Majalisar Dattawa — David Mark da Ken Nnamani da tsoffin gwamnonin Sakkwato da Kuros Riba — Aminu Waziri Tambuwal da Donald Duke.