✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa

Gwamnonin sun yi addu'ar Allah Ya jiƙanta, Ya kuma bai wa iyalanta haƙurin rashinta.

Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta.

Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta hanyar riƙe kyawawan halayenta na gaskiya da nagarta.

Gwamnan Gombe, ya kuma miƙa ta’aziyyar gwamnatinsa da mutanen jiharsa, ta hanyar addu’ar Allah Ya gafarta mata, Ya kuma sa Aljanna Firdausi ta zama makomarta.