✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin ’yan kwadago sun kauracewa zama da Gwamnatin Tarayya

A gobe Talata ne NLC za ta fara yajin aikin gargadi na kwana biyu.

Shugabannin Kungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) sun kaurace wa taron da ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ya kira da nufin dakile yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da kungiyar kwadagon ta shirya shiga.

Aminiya ta ruwaito cewa, shugaban kungiyar (TUC) ne kawai, Festus Osifo, ya halarci taron da aka shirya yi da misalin karfe 3 na rana, wanda aka fara da misalin karfe 5:32 na yamma.

A halin yanzu dai taron ya shiga wani zama na sirri, inda ministan ya hana ‘yan jarida damar shiga taron.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce NLC ta bayyana cewa ma’aikata a fadin kasar nan su fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu daga ranar Talata 5 ga watan Satumba saboda halin kuncin da ‘yan Najeriya ke ciki a fadin kasar nan.

Aminiya ta ruwaito a baya cewa Lalong a wata zantawa da manema labarai da ya yi a baya, ya bayyana cewa har yanzu bai gana da shugabannin NLC ba, saboda har yanzu bai samu isassun bayanai daga ɓangarorin da abin ya shafa ba.

Da yake jawabi a wajen taron, Lalong ya yi kira na musamman ga shugabannin TUC da NLC da su sake nazari kafin shiga yajin aikin da suke shirin tsunduma a ranar Talata.