Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta miƙawa Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON kuɗi sama da Naira biliyan 6 a matsayin kuɗin jigilar maniyyatan jihar na 2025 na zuwa Saudiyya.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Labbo a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse, ya ce hukumar ta raba tare da sayar da kason kujerun aikin Hajji sama da 1,000 na jihar ga ƙananan hukumomi 27 ga mahajjata.
Umar Labbo ya bayyana cewa, hukumar ta kammala shirye-shiryenta da suka haɗa da biza ga maniyyatan jihar, inda a yanzu ake jiran tashin jirgi na farko daga jihar da zarar lokacin ya yi.
Don haka ya shawarci maniyyatan jihar da su kasance wakilan ƙasar nagari ta hanyar gujewa abubuwan da za su ɓata sunan jihar da ƙasa baki ɗaya yayin da suke ƙasa mai tsarki.
Babban daraktan ya kuma shawarci alhazai da su yi amfani da ilimin da suka samu a aikin Hajji a kowane mataki, ya kuma shawarce su da su riƙa yin haƙuri a matsayin abokan aikinsu a duk tsawon wannan aiki, ya buƙace su da su bi ƙa’idojin da hukumar ta tanadar a duk lokacin gudanar da aikin.
Ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa yadda yake ci gaba da baiwa hukumar tallafi, wanda ya sa hukumar ta ɓullo da tsare-tsaren buƙatun alhazai daban-daban domin samun walwala da kariya.
