Gwamnoni Arewacin Najeriya sun yi ittifakin yin amfani da ‘yan banga da maharba wajen zakulo bayanan sirri da za a yi amfani da su wajen kawo karshen kashe-kashe a yankin.
A taron da kungiyar gwamnonin ta gudanar a kafar Teleconferencing, sun nuna alhilinsu kan kashe-kashen da ke ta faruwa a yankunan Katsina da Zamfara da Sokoto da sauran wuraren.
Sanarwar bayan taron ta bayyana cewar matsayar da gwamnonin suka dauka sun hada da: ” Nada tsayayyen kwamitin tsaro a Arewa da zai yi aiki da jami’an tsaro domin tabbatar da matakan tsaro a yankin.
“Gwamna Yahaya Bello na Kogi zai jagorance shi sai kuma gwamnonin Zamfara da Gombe a matsayin mambobi”.
- Dalilan dacewar Buhari ya kori hafsoshin tsaro
- Manyan hafsoshin tsaro sun gaza, ba su da uzuri —Buhari
- ‘Yan bindiga: Gwamnonin Arewa za su yi taron dangi
Sanarwar ta ce gwamnonin sun kafa wani kwamitin da shugaban kungiyar Gwamna Simon Lalong na Filato zai jagoranta sai kuma gwamnonin Sokoto da Adamawa da Neja, a matsayin mambobi.
Kwamitin zai kuma tuntubi sarakuna da malaman addini da kuma shugabbanin al’umma domin ganin an fadada hanyoyin tabbatar da ganin an dakile matsalolin tsaro a yankin.
“Za su yi amfani da ‘yan banga da maharba da masu sa ido a cikin al’umma a tsarin tsaro na yankin domin zakulo bayanan sirri da za a yi amfani da su wajen dakile rashin tsaro.”
Gwamnonin sun tausaya wa wadanda bala’in ya auka wa da kuma ba su kwarin gwiwar cewa gwamnatocin jihohi da ta tarayya na bakin kokarin ganin an shawo kan rashin tsaro da kuma magance matsaloli na yau da kullum da fitintunun suka janyo wa wadanda abin ya shafa.
Daga karshe suka roki jami’an tsaro da su mayar da hankali wajen ganin sun kawo karshen kashe-kashe ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a kasar.